Akwai yiwuwar APC ta hana Amaechi, Ngige, Malami da wasu Ministoci yin takara

Akwai yiwuwar APC ta hana Amaechi, Ngige, Malami da wasu Ministoci yin takara

  • Akwai shakku a game da hukuncin da kotu za ta yi a game da aiki da sabuwar dokar zaben Najeriya
  • Wani sashen dokar zaben ya ce dole sai an ajiye kujerar siyasa sannan za a iya shiga takara a jam’iyya
  • Daga baya kotu ta yi watsi da wannan dokar, amma idan aka soke hukuncin, za a iya samun matsala

Abuja - Alamu masu karfi na nuni ga cewa jam’iyyar APC za ta haramta wadanda ke cigaba da rike da mukaman siyasa yin takara a zabe mai zuwa.

Wani dogon rahoto da ya fito daga jaridar Punch ya bayyana cewa jam’iyyar APC mai mulki ba za ta dauki cacar da zai sa tayi asarar neman takara ba.

Sashe na 84 (12) na dokar zabe ya wajabtawa masu rike da mukaman gwamnati sauka daga kujerunsu kafin su iya yin takara a karkashin jam’iyya.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Kotu ta kori tsohon kakakin majalisa Dogara daga majalisar wakilai

Kawo yanzu akwai Ministoci biyu, na sufuri da na kwadago; Rotimi Amaechi da Chris Ngige da suke niyyar neman tikitin takarar shugaban kasa a APC.

Sannan kuma ana zargin Ministan shari’a, Abubakar Malami (SAN) ya na da burin yin takarar gwamna a jihar Kebbi, duka ba su ajiye mukamansu ba.

Wani da ke rike da kujera majalisar NWC ya shaidawa jaridar cewa abin da ya dace shi ne Ministocin su yi murabus kafin shiga zaben fitar da gwani.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wasu Ministoci
Buhari a taron FEC Hoto: www.vanguardngr.com
Asali: UGC

Shi kuma wani babba a jam’iyyar ya bayyana cewa za su jira hukuncin kotu kafin su dauki matsaya, hukuncin Alkalin zai yi tasiri wajen daukar mataki.

Kwanaki sakataren yada labarai na APC na kasa, Felix Morka, ya ce za su tabbatar duk wani mai neman kujerar siyasa ya sauka daga mukamin da yake kai.

Kara karanta wannan

2023: Shehu Sani ya hango yadda APC da PDP za su zabi 'yan takarar shugaban kasa

Amma har zuwa yanzu ba a ji wani Minista ko Jakada da ya rubuta murabus ba. A jihohi kuwa, Kwamishinoni da sauran masu mukamai su na ta barin ofis.

An yi gaba, an yi baya

Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi ‘yan majalisa su goge sashe na 84 (12) na sabuwar dokar zaben, sai dai sam ba su karbi wannan roko da ya gabatar ba.

A karshe aka ji wani Lauya, Nduka Edede ya dumfari wani kotu da ke zama a garin Umuhia da sunan cewa sharadin ya saba doka, a karshe aka yi hakan.

Evelyn Anyadike ta ce sashen ya saba dokar kasa, don haka ta bukaci AGF ya gyara dokar zaben. yanzu dai an daukaka kara, ana sauraron hukuncin da za ayi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel