Karin bayani: Shugaba Buhari ya shiga ganawa da dan takarar shugaban kasa a PDP, Tambuwal

Karin bayani: Shugaba Buhari ya shiga ganawa da dan takarar shugaban kasa a PDP, Tambuwal

  • Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja
  • Babu wani abu na tattaunawarsu da manema labarai suka sani, wanda ya zo ne bayan da dattawan jam’iyyar PDP na Arewa suka zabi ‘yan takarar shugaban kasa a 2023
  • Koma dai menene, Gwamna Tambuwal ya ce yana tafiya ne da burinsa na zama shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa

Abuja - Fadar shugaban kasa ta fitar da sanarwa dauke da hotuna cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal sun gana a fadar shugaban kasa da ke Aso Rock Villa, Abuja.

Tambuwal dai na daya daga cikin 'yan takarar shugaban kasa na jam'iyyar adawa ta PDP da ke da burin gaje kujerar Buhari a zaben 2023 mai zuwa.

Kara karanta wannan

Ramadan: Tinubu, Nyako da jiga-jigan APC 15 da za su yi buda baki tare da Buhari a yau

Ganawar ta Buhari da Tambuwal na zuwa ne kwanaki kadan bayan da shirin yarjejeniyar jam’iyyar PDP da aka tsara na ‘yan takarar shugaban kasa hudu a Arewa ya fada cikin rudani.

Shugaba Buhari ya gana da Tambuwal
Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya shiga ganawa da dan takarar shugaban kasa a PDP, Tambuwal | Hoto: @NigeriaGov
Asali: Twitter

‘Yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP da ke cikin wannan shiri na yarjejeniya sun hada da Tambuwal; Gwamnan Bauchi Bala Mohammed; Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da tsohon Manajan Darakta na Bankin Duniya na FsB, Mohammed Hayatu-Deen.

Rahotanni bayan yarjejeniyar sun nuna cewa, wasu 'yan takarar jam'iyyar PDP sun nuna adawa da sahirin, kana sun yi Allah wadai dashi.

Kalli hotunan ganawar tasu:

Tikitin shugaban kasa: PDP za ta tantance Atiku, Saraki, Tambuwal da wasu yan takara 14 a ranar Juma’a

A baya kun ji cewa, a ranar Juma’a mai zuwa ne jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) za ta tantance yan takara 17 da ke fafutukar mallakar tikitin shugaban kasa na jam’iyyar gabannin zaben 2023.

Kara karanta wannan

Kotun Ƙoli ta yanke hukuncin ƙarshe kan halascin ɗan takarar APC a zaben gwamnan Anambra

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Cif David Mark, shine shugaban kwamitin mutum tara da za su gabatar da shirin tantance yan takarar, jaridar The Nation ta rahoto.

Shugaban kasa a 2023: Ban yarda da tsarin karba-karba ba – Gwamna Bala Mohammed

A wani labari, gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya bayyana cewa bai yarda da tsarin karba-karba ba gabannin zaben shugaban kasa na 2023 amma maimakon haka ya ce abun da ya kamata a mayar da hankali a kai shine neman shugaba da zai iya jagorantar Najeriya.

Gwamna Bala ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talbijin na Channels a shirin ‘Sunday Politics’.

Hakan na zuwa ne yan kwanaki bayan kungiyar dattawan arewa ta zabe shi da tsohon shugaban majalisar dattawa a matsayin yan takarar yarjejeniya na jam’iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel