Masari ya nada Muntari Lawal a matsayin mukaddashin sakataren gwamnatin jihar Katsina

Masari ya nada Muntari Lawal a matsayin mukaddashin sakataren gwamnatin jihar Katsina

  • Gwamna Aminu Bello Masari ya nada Alhaji Muntari Lawal a matsayin mukaddashin sakataren gwamnatin jihar Katsina
  • Hakan ya biyo bayan ajiye aiki da sakataren gwamnatin jihar, Dr Mustapha Inuwa, ya yi domin ya samu damar shiga takarar kujerar gwamna a zaben 2023
  • Ana tsammanin Masari zai yi karin nade-nade a yan kwanaki masu zuwa domin cike gurbin da wasu mambobin majalisarsa suka bari

Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya nada Alhaji Muntari Lawal a matsayin mukaddashin sakataren gwamnatin jihar.

Daily Trust ta rahoto cewa sabon nadin na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun darakta janar na labaran gwamnan, Al-Amin Isa.

Nadin nasa ya biyo bayan murabus din sakataren gwamnatin jihar, Dr Mustapha Inuwa, wanda ya shiga takarar kujerar gwamnan jihar a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: kwamishinan gwamna Zulum ya yi murabus, zai tsaya takara kujerar yankinsu

Masari ya nada Muntari Lawal a matsayin mukaddashin sakataren gwamnatin jihar Katsina
Masari ya nada Muntari Lawal a matsayin mukaddashin sakataren gwamnatin jihar Katsina Hoto: Vanguard
Asali: Facebook

Kafin nadin nasa a sabon mukamin, Lawal ya kasance shugaban ma’aikatan gwamnan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Vanguard ta rahoto cewa nadin nasa ya fara aiki ne a nan take.

A yan kwanaki masu zuwa, ana sa ran gwamnan na jihar Katsina zai yi Karin nade-nade domin cike gurbin da mambobin majalisarsa da ke shirin tsayawa takarar kujerun siyasa a zabe mai zuwa suka bari.

Shirin 2023: Ali Ndume, Suswam da jiga-jigai 5 da ke aiki don ganin wasu 'yan takara sun gaji Buhari

A gefe guda, mun ji cewa yayin da Najeriya ke shirye-shiryen babban zabenta na 2023, wasu yan siyasa sun nada wadanda za su jagoranci yakin neman zabensu.

Yan siyasa a fadin jam’iyyun siyasa daban-daban suna ta tallata ubannin gidansu domin ganin sun zama yan takarar jam’iyyunsu mabanbanta.

Kara karanta wannan

Katsina: Sakataren gwamnati ya yi murabus daga kan mukaminsa, ya shiga takara a 2023

A cikinsu akwai manyan sanatoci, gogaggun ‘yan siyasa da kuma tsofaffin masu rike da mukaman siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng