Shirin 2023: Ali Ndume, Suswam da jiga-jigai 5 da ke aiki don ganin wasu 'yan takara sun gaji Buhari

Shirin 2023: Ali Ndume, Suswam da jiga-jigai 5 da ke aiki don ganin wasu 'yan takara sun gaji Buhari

  • Tuni yan takarar shugaban kasa na manyan jam’iyyun siyasar kasar biyu a zaben 2023 suka kafa kungiyoyin kamfen dinsu
  • Daga jam’iyyar APC mai mulki har PDP mai adawa a kasar suna da tarin yan takara da ke son mallakar tikitin shugaban kasa
  • Yan takarar sun nutsu sun zabi jagororin kamfen dinsu tare da tuntubar mutane da dama

Abuja – Yayin da Najeriya ke shirye-shiryen babban zabenta na 2023, wasu yan siyasa sun nada wadanda za su jagoranci yakin neman zabensu.

Yan siyasa a fadin jam’iyyun siyasa daban-daban suna ta tallata ubannin gidansu domin ganin sun zama yan takarar jam’iyyunsu mabanbanta.

A cikinsu akwai manyan sanatoci, gogaggun ‘yan siyasa da kuma tsofaffin masu rike da mukaman siyasa.

Shirin 2023: Ali Ndume, Suswam da jiga-jigai 5 da ke aiki don ganin wasu 'yan takara sun gaji Buhari
Shirin 2023: Ali Ndume, Suswam da jiga-jigai 5 da ke aiki don ganin wasu 'yan takara sun gaji Buhari Hoto: @NGRSenate
Asali: Twitter

Legit Hausa ta zakulo maku su kamar haka:

Kara karanta wannan

Tikitin shugaban kasa: PDP za ta tantance Atiku, Saraki, Tambuwal da wasu yan takara 14 a ranar Juma’a

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

1. Sanata Kabiru Gaya (Yakin neman zaben Yemi Osinbajo campaign)

Sanata Kabiru Ibrahim Gaya mai wakiltan yankin Kano ta kudu shine babban daraktan yakin neman zaben Yemi Osinbajo wanda aka sani da ‘The Progressive Project’.

Ana sanya ran nadin gogaggen dan siyasan zai taimakawa mataimakin shugaban kasar wajen samun goyon bayan wakilan APC a arewa maso yamma gabannin zaben fidda gwanin jam’iyya.

2. Sanata Gabriel Suswam (Yakin neman zaben Udom Emmanuel)

Tsohon gwamnan jihar Benue, Sanata Gabriel Suswam, shine shugaban kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na Gwamna Udom Emmanuel.

Ana sanya ran Suswam zai yi amfani da gogewarsa wajen taimakawa gwamnan na jihar Akwa Ibom don ya cimma manufarsa na lashe tikitin shugaban kasa na PDP gabannin zaben 2023.

3. Abdulmumin Jibrin (Yakin neman zaben Bola Tinubu)

Abdulmumin Jibrin, tsohon dan majalisar wakilai daga jihar Kano shine babban daraktan kungiyar yakin neman zaben Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Zaɓen 2023: Kada Ka Ruɗa Ƴan Najeriya, Ƙungiya Ta Ja Kunnen Atiku

Jibrin ya jajirce wajen tallata ubangidan nasa a wajen mambobin APC dama yan Najeriya baki daya a cikin yan makonnin da suka gabata.

4. Sanata Tunde Ogbeha (Yakin neman zaben Aminu Tambuwal)

Sanata Tunde Ogbeha shine shugaban kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na Aminu Waziri Tambuwal.

Ogbeha mai shekaru 75 ya kasance gogaggen dan siyasa kuma tsohon janar mai ritaya daga jihar Kogi; wanda ya kasance gwamnan jihar Akwa Ibom a mulkin soji na Janar Ibrahim Babangida. Daga baya ya shiga majalisar dattawan Najeriya.

5. Sanata Jonathan Zwingina (Yakin neman zaben Yahaya Bello)

Haifaffen dan jihar Adamawa Sanata Jonathan Zwingina ya kasance shugaban yakin neman zaben Yahaya Bello.

Zwingina, tsohon mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, yay i aiki a matsayin darakta-janar na kungiyar kamfen din Moshood Abiola a 1993. Ana ganin nadin nasa a matsayin babban dabara ga gwamnan na jihar Kogi.

Kara karanta wannan

Jerin yan takarar shugaban kasa 5 da suka ce Ubangiji ne ya kira su domin yin takara

6. Cif Raymond Dokpesi (Yakin neman zaben Atiku Abubakar)

Tsohon shugaban kamfanin sadarwa ta Daar, Raymond Dokpesi, ya kasance shugaban kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar.

Dokpesi ya kasance dan gaba a kungiyar kamfen din Atiku, inda yake tallata ubangidansa da kuma dagewa a kan tsarin karba-karba a PDP.

7. Sanata Ali Ndume (Yakin neman zaben Chibuike Amaechi)

Sanata Mohammed Ali Ndume shine darakta janar na kungiyar yakin neman zaben Rt Hon Chibuike Amaechi.

Ndume wanda ya kasance shugaban kwamitin majalisar dattawa ya bayyana a kwanan nan cewa shugabancin Amaechi aiki ne nasa na gashin kansa kuma zai tabbatar da gwanin tsohon gwamnan ya zama shugaban kasar Najeriya na gaba.

Bayan ganawa da Buhari, wani gwamnan APC ya ayyana tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023

A wani labari na daban, gwamnan jihar Kuross Riba, Ben Ayade, ya ce zai nemi takatar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 bayan shugaba Buhari ya amince masa ya yi hakan.

Kara karanta wannan

2023: Shehu Sani ya hango yadda APC da PDP za su zabi 'yan takarar shugaban kasa

Gwamnan ya gana da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ranar Talata a Aso Villa dake Abuja, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Da yake jawabi ga manema labarai Bayan gana wa da shugaban ƙasan, Ayade ya ce Buhari ya bukace shi ya nemi shawarar mutane kan lamarin yayin da zai sa masa ido ya gani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel