Da Dumi-Dumi: Bayan ganawa da Buhari, wani gwamnan APC ya ayyana tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023

Da Dumi-Dumi: Bayan ganawa da Buhari, wani gwamnan APC ya ayyana tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023

  • Gwamna Ben Ayade na jihar Kuros Riba ya ce shugaban ƙasa Buhari ya amince masa ya nemi shugaban ƙasa a 2023
  • Jim kaɗan bayan gana wa da Buhari a Abuja, gwamnan ya ce zai fito takara ne amma ba wai dole shi za'a ba tikiti ba
  • Ya ce idan har jam'iyyar APC ta ga dacewar bai wa Jonathan takara don samun nasara to a shirye yake ya janye

Abuja - Gwamnan jihar Kuross Riba, Ben Ayade, ya ce zai nemi takatar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 bayan shugaba Buhari ya amince masa ya yi hakan.

Gwamnan ya gana da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ranar Talata a Aso Villa dake Abuja, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Da yake jawabi ga manema labarai Bayan gana wa da shugaban ƙasan, Ayade ya ce Buhari ya bukace shi ya nemi shawarar mutane kan lamarin yayin da zai sa masa ido ya gani.

Kara karanta wannan

N-Power: Bayan umarnin Buhari zamu ƙara daukar matasa 13,823 a rukunin C a wannan jihar, Sadiya Farouq

Shugaba Buhari tare da gwamna Ben Ayade
Da Dumi-Dumi: Bayan ganawa da Buhari, wani gwamnan APC ya ayyana tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023 Hoto: Buhari Sallau/facebook
Asali: Facebook

Ko wane mataki Ayade zai ɗauka Idan APC ta yanke ba Jonathan takara?

Game da raɗe-raɗin APC na shirya tsayar tsohon shugbaan ƙasa, Goodluck Jonathan, Ayade ya ce ya na matukar girmama shi, idan APC ta ɗauki matakin ba shi takara zai goya masa baya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa da Daily Trust ta ruwaito, gwamnan ya ce:

"Ina da yaƙinin shugabannin mu na jam'iyya zasu ɗauki matakin da zai kai mu ga nasara, dan haka idan kun fahimce ni, ni kawai ina ɗaya daga cikin iyali ne, ina bayan Buhari, kuma ina neman takara."
"A duk lokacin da jam'iyyar mu ta ga cewa Jonathan ne zai iya kaimu ga nasara, zan maida baki ɗaya goyon bayana a kan sa na taimake shi."
"Ba na siyasar yaƙi, duk wanda ya san yadda na zama gwamna, na kai wannan matsayin ne saboda goyon bayan wanda gwamna ke so, sai a kai sa'a na zama nine ɗan takara. Don haka zan koma bayan wanda shugaban ƙasa ke so."

Kara karanta wannan

Hotuna: Asiwaju Bola Tinubu ya shiga jerin yan Najeriya da suka garzaya aikin Umrah

A wani labarin kuma Wasu masoyan shugaba Buhari sun koma bayan Kwankwaso ya gaji shugaban ƙasa a 2023

Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya samu gagarumin goyon baya a shirinsa na gaje Buhari a 2023.

Wata ƙungiyar yan a mutun shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ta tabbatar da goyon bayanta ga jagoran Kwankwasiyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel