Jerin yan takarar shugaban kasa 5 da suka ce Ubangiji ne ya kira su domin yin takara

Jerin yan takarar shugaban kasa 5 da suka ce Ubangiji ne ya kira su domin yin takara

  • Tseren neman shugabancin kasar na kara zafi yayin da karin yan siyasa ke nuna sha’awarsu sosai a kan kujerar
  • Gabannin zaben, akwai yan takarar da suka bayyanawa duniya cewa Ubangiji ne ya kira su domin shiga tseren
  • Wadannan yan takara sun hada da gwamnoni da ministoci masu ci, wadanda suka kasance mambobin manyan jam’iyyun siyasar kasar biyu

Fafutukar neman darewa kujerar shugaban kasa na kara kamari gabannin 2023 yayin da karin yan takara ke ci gaba da zawarcin yan Najeriya domin su jefa masu kuri’unsu wanda shine zai kai su matsayin.

Da dama daga cikinsu ba wai kawai suna magana ne kan gogewarsu ba, maimakon haka suna goyon bayan takararsu da abubuwan da mutane ke tsammani.

Sai dai yan Nakeriya sun shirya ma abun yayin da takarar babbar kujera ta daya a kasar ke kara zafi.

Kara karanta wannan

'Dana mulkin da nayi lokacin da Buhari ke jinya yasa nike ganin na cancanci zama shugaban kasa: Osinbajo

Ana saura yan watanni kafin zaben na 2023, wasu yan siyasa sun bayyana cewa Ubangiji ne ya nemi su shiga takarar zaben shugaban kasar, The Cable ta rahoto.

Ga jerin yan siyasar da suka ce Ubangiji ne ya nemi su yi takarar shugaban kasa a 2023.

1. David Umahi

Jerin yan takarar shugaban kasa 5 da suka ce Ubangiji ne ya kira su domin yin takara
Jerin yan takarar shugaban kasa 5 da suka ce Ubangiji ne ya kira su domin yin takara Hoto: David Nweze Umahi
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A watan Jamairu, gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya ayyana aniyarsa ta son takarar kujerar shugaban kasa a babban zaben 2023 bayan wata ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Umahi ya ayyana aniyar tasa ne awa 24 bayan Bola Tinubu, jagoran APC na kasa, ya ce ya sanar da shugaban kasar kudirinsa na son takara a 2023.

Da yake magana kan takarar tasa, gwamnan na Ebonyi ya ce ya ayyana kudrinsa ne bayan Ubangiji ya yi masa magana kan haka.

“Rayuwa tana da karfi sosai kuma Ubangiji ya yi magana da ni. Don haka ci gaba ne kuma ina tsammanin na yi magana ne a lokacin da Allah ya ce in yi magana. Abin da na yarda da shi kenan."

Kara karanta wannan

2023: Shehu Sani ya hango yadda APC da PDP za su zabi 'yan takarar shugaban kasa

2. Chris Ngige

Jerin yan takarar shugaban kasa 5 da suka ce Ubangiji ne ya kira su domin yin takara
Jerin yan takarar shugaban kasa 5 da suka ce Ubangiji ne ya kira su domin yin takara Hoto: Ngige Nwachukwu
Asali: Facebook

A ranar 16 ga watan Afrilu, Ngige, ministan kwadago da daukar ma’aikata, ya fada ma magoya bayansa cewa Ubangiji ya yi magana da shi don ya ayyana aniyarsa ta son yin takarar shugaban kasa a 2023.

Ya ce:

“Ina so in tabbatar muku da cewa tsawon lokaci, mun kawo karshen shi a daren jiya. Kuma a cikin wannan lokaci, mun yi magana da Ubangiji; mun yi azuminmu; mun yi magana da Ubangiji da mala'iku sai Ubangiji ya mayar mana da martani. Ubangiji ya yi magana da ni.”

Kwanaki uku bayan nan, sai ministan kwadagon ya ayyana kudirinsa na yin takarar shugaban kasa a zaben 2023 a hukumance.

3. Dele Momodu

Jerin yan takarar shugaban kasa 5 da suka ce Ubangiji ne ya kira su domin yin takara
Jerin yan takarar shugaban kasa 5 da suka ce Ubangiji ne ya kira su domin yin takara Hoto: Dele Momodu
Asali: Facebook

A watan Janairu, Momodu, dan jarida kuma mawallafin mujallar Ovation Magazine, ya shiga takarar shugaban kasa.

Da yake magana kan kudirinsa, mawallafin ya ce Allah ne ya zabe shi domin ya zama shugaban kasar Najeriya yayin da ya yi alkawarin gyara kasar.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Har yanzu ina shawarar takara, ku dakace ni: Goodluck Jonathan

4. Olasupo Akinola

Jerin yan takarar shugaban kasa 5 da suka ce Ubangiji ne ya kira su domin yin takara
Jerin yan takarar shugaban kasa 5 da suka ce Ubangiji ne ya kira su domin yin takara Hoto: BBC News Pidgin
Asali: Facebook

Olasupo Akinola, matashin Malamin addini dan shekara 40 ya ayyana niyyar shiga takarar neman kujeran shugaban kasar Najeriya a zaben 2023.

Ya ce Allah ne ya umurce shi da ya shiga tseren kujerar domin kawo karshen matsalolin da suka addabi kasar.

Ya yi alkawarin inganta Najeriya ga talakawan kasa tare da yin kira ga shugabannin da suka gabata da su mara masa baya.

5. Sau uku Ubangiji na kirana, ya ce Atiku ne zai gaji Buhari a 2023, inji Dino Malaye

Jerin yan takarar shugaban kasa 5 da suka ce Ubangiji ne ya kira su domin yin takara
Jerin yan takarar shugaban kasa 5 da suka ce Ubangiji ne ya kira su domin yin takara Hoto: Dino Melaye, Atiku Abubakar Hausa
Asali: Facebook

Koda dai Dino Melaye, tsohon sanata mai wakiltan Kogi ta yamma baya takarar shugaban kasa, Meaye ya ce Ubangiji ya kira sa sau uku sannan yana fada masa cewa Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa ne zai zama shugaban kasar Najeriya na gaba.

Ya ce:

“Da ikon Allah, yayin da nake mika lasifika ga Cif Raymond Dokpesi domin gabatar da cikakken fom dinnan ga sakataren gudanarwa na kasa, ina so na bayyana cewa da yawa daga cikinmu idan muka yi kira ga Ubangiji, Ubangiji ba Ya kin amsa kiranmu.

Kara karanta wannan

Dole ka tsaya takara: Masoya Jonathan sun mamaye ofishinsa, suna neman gafara

“Idan muka kira shi, yana amsa kiranmu. Kuma ya kira ni sannan ya ce dani Dino, nace na’am ya Ubangiji na. ya sake kirana a karo na biyu, nace na’am ya Ubangijina. Ya kira ni a karo na uku, sannan ya ce: “Atiku zai zama shugaban kasar Najeriya.”

N50m na ware tun farko, Minista ya fadi hanyar da zai tara N100m na sayen fam a APC

A wani labari, jam’iyyar APC mai mulki ta yanke kudin fam din shiga zaben takarar shugaban kasa a kan Naira miliyan 100 a zabe mai zuwa da za ayi a 2003.

Premium Times ta rahoto Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige ya na cewa ya yi lissafin zai kashe Naira miliyan 50 ne wajen sayen fam.

Asali: Legit.ng

Online view pixel