Shugaban kasa a 2023: Idan na sayi fom din miliyan N100 za a ce ni barawo ne – Adamu Garba

Shugaban kasa a 2023: Idan na sayi fom din miliyan N100 za a ce ni barawo ne – Adamu Garba

  • Adamu Garba ya bayyana dalilinsa na neman takarar shugaban kasa maimakon ya fara daga karamar kujera
  • Malam Adamu ya kuma koka a kan tsawwala kudin fom da jam'iyyarsa ta APC ta yi wanda ya kai naira miliyan 100
  • Ya bayyana cewa idan har ya sayi fam din wadanda ke tare da shi za su ce shi barawo ne ganin cewa shi ma'aikaci ne a kamfani mai zaman kansa

Daya daga cikin masu neman mallakar tikitin shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress a zaben 2023, Adamu Garba, ya koka kan tsawwala kudin fom din takarar kujerar da jam’iyyarsa ta yi.

A wata hira da ya yi da sashin Hausa na BBC, matashin dan siyasar ya ce a matsayinsa na wanda ke aiki a kamfanin mai zaman kansa, ba shi da halin sayen fom din takarar shugaban kasa na naira miliyan 100 sai dai idan an yi masa karo-karo.

Kara karanta wannan

Martanin yan Najeriya kan sabuwar wakar sukar gwamnatin Buhari da Rarara ya yi

Ya ce idan ma ya siya toh lallai wadanda ke tare da shi cewa za su yi shi din barawo ne.

Shugaban kasa a 2023: Idan na sayi fom din miliyan N100 za a ce ni barawo ne – Adamu Garba
Shugaban kasa a 2023: Idan na sayi fom din miliyan N100 za a ce ni barawo ne – Adamu Garba Hoto: @ArewareportersAR
Asali: Facebook

Dan siyasar ya kuma kara da cewar ya fito takarar shugaban kasa ne domin kawo sauyi a kasar ganin cewa sauyi ba zai samu sosai ba idan mutum bai hau kan wannan babban kujerar ba.

Da aka tambaye shi kan dalilin da yasa ba zai nemi karamar kujera ba sai ta shugaban kasa, Adamu ya ce:

“Wato matsalar kasar ne idan ka duba za ka ga cewa akwai abun da ake kira ‘system issue’ wato tsarin kasar shine ake da matsala da shi ba wai shugabanci ba. Misali idan har mutum ya ce zai karbi kujera na kasa ko kansila, ko Ciyaman, ko kuma misali a ce dan majalisar jiha ko dan majalisar tarayya ko sanata ko gwamna banda dai ta shugaban kasa, duk gabaki daya wadannan kujerun an tsara tsarinsu ne a kan su tawo Abuja su zo su karbi abun da za su sa a aljihu, wannan shine babbar matsala.

Kara karanta wannan

Jigon APC ga 'yan takara: Kunsan ba ku da N100m me ya kai ku takara a jam'iyyar APC

"Kuma mu tsarin da muka zo da shi mun zo da wani tsari ne wanda za a kirkiro da yadda za a yi kowani bangare ya kawo abun da za a hada a Abuja ta ci gaba da aiwatar da yadda take tafiyar da lamarinta.
“Ba wai a zo ne a dauki kudi na mai a raba ba, a’a yadda za a yi kowa ya kawo wani abu da za a samu ci gaban kasa, babu yadda za a yi a samu wannan chanji sai an hau kan wannan babban kujerar ta shugaban kasa. Saboda kaso 80 cikin 100 na karfin mulkin Najeriya na kan wannan kujera, don haka idan ba mutum ya hau wannan kujera ba babu gyara da zai yi. Kawai shima yana bukata ne ya samu dama ya hau a turo masa abun da aka turo masa ya raba ya samu na sawa a aljihu yayi amfani da sauran idan har zai yi aiki nagari.

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar APC ta hana Amaechi, Ngige, Malami da wasu Ministoci yin takara

“Toh shiyasa tunda mu muna da bukatar a kawo tsari gabaki daya na yadda harkar kasar ke tafiya, babu wani dama da zamu iya yi sai an hau wannan kujera na shugaban kasa. Kuma shi wannan shiri da na yi sama da shekaru 17 zuwa 19 shiri da nayi na yi shi ne na zama shugaban kasar Najeriya saboda da abubuwa da muka shirya abubuwa ne saboda gyara da za a iya kawowa sai ta ofishin shugaban kasa ba kasa da haka ba. Shiyasa nake neman takarar ofishin shugaban kasa.”

Ya ci gaba da cewa:

“Na biyu wannan ofishin, ofishi ne na jama’a ba ofishi ne wai ni zan yi aiki da shi ba kuma an dauki kudi kimanin naira miliyan 100 an sa a matsayin wanda za a yi amfani da shi wajen siyar wannan fam din.
“Miliyan 100 ba karamin kudi bane. Yanzu haka mutanen da nake tare da su idan suka ga na tattara naira miliyan 100 na je na biya kudin ai kowa zai ce ni barawo ne a matsayina na ma’aikaci wanda yake aiki a karkashin kamfani mai zaman kansa ba aikin gwamnati ba.

Kara karanta wannan

Yana ta wasu bakin abubuwa kafin mutuwarsa – Hadimin Alaafin ya bayyana yadda karshensa ya kasance

“Ma’aikatan gwamnati kansu idan kace kai shugaban kasa ne a Najeriya idan dai albashinka kawai ka ce za ka dogara da shi sai ka tara kusan shekara bakwai kafin za ka hada naira miliyan 100. Ka ga duk mutumin da ya ce ya dauki naira miliyan 100 a halin yanzu ya siya fom ka ga idan dai ba karo-karo aka yi masa ba ta kan yiwu sata yake yi, shiyasa muke neman karo-karo a hada karfi da karfe.”

Matashin da zai yi takarar Shugaban kasa a APC, ya nemi ayi masa karo-karon kudin fam

A baya mun ji cewa Malam Adamu Garba II ya fara yakin neman zaben shugaban kasa gadan-gadan, ya yi kira ga mutane su taimakawa wannan tafiya da ya dauko.

Legit.ng Hausa ta fahimci Adamu Garba II ya saki lambobin akawun na banki ga masoyansa domin a taimaka masa da kudin da zai yanki fam a APC.

Kara karanta wannan

Jerin yan takarar shugaban kasa 5 da suka ce Ubangiji ne ya kira su domin yin takara

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng