Yana ta wasu bakin abubuwa kafin mutuwarsa – Hadimin Alaafin ya bayyana yadda karshensa ya kasance

Yana ta wasu bakin abubuwa kafin mutuwarsa – Hadimin Alaafin ya bayyana yadda karshensa ya kasance

  • Rahotanni sun kawo cewa Marigayi sarkin Oyo ya ki yarda a fitar da shi kasar waje domin yin jinya
  • A cewar daya daga cikin hadimansa, marigayi sarkin ya fi so likitocin Najeriya su duba lafiyar shi
  • Hadimin ya kuma bayyana yadda ranakun karshe suka kasancewa basaraken a duniya bayan an kai shi asibitin koyarwa na jami’ar Afe Babalola

Oyo - Wani haifaffen garin Oyo, wanda ya kasance hadimi ga Oba Lamidi Adeyemi, ya ce marigayi sarkin Oyo ya ki yarda a fita da shi kasar waje a lokacin da ya kwanta ciwo kafin mutuwarsa.

Hadimin sarkin wanda ya zanta da jaridar The Cable, ya ce sarkin ya gwammaci a yi jinyarsa a Najeriya sannan yana ta wasu bakin abubuwa a kwanakin karshe da zai kwanta dama.

Kara karanta wannan

Sarkin Oyo ya hango mutuwarsa, ya fada mana cewa magabatansa sun yi kira - Hadimarsa

Yana ta wasu bakin abubuwa kafin mutuwarsa – Hadimin Alaafin ya bayyana yadda karshensa ya kasance
Yana ta wasu bakin abubuwa kafin mutuwarsa – Hadimin Alaafin ya bayyana yadda karshensa ya kasance Hoto: Dailytrust.com
Asali: UGC

Ya ce:

“Da ya kwanta rashin lafiya, an bukaci da ya tafi Turai don ganin likita. An bayar da shawarar ne saboda yadda hannaye da kafafuwansa suka kumbura.
“Hakazalika jikinsa yana ta saki. Amma ya ki yarda da shawarar. Ya ce akwai kwararrun likitoci a Najeriya da za su iya duba shi. Don haka sai muka yanke shawarar kai shi asibitin koyarwa na Afe Babalola da ke Ado-Ekiti. Mamallakin asibitin abokin sarkin ne don haka sai muka kira shi sannan ya ce mu kawo shi cikin gaggawa.”

Hadimin sarkin ya ce da farko ya fada masa a kunne cewa akwai abubuwan da zai so ya kammala idan yana da sauran lokaci a rayuwarsa.

Ya ce:

“A daya daga cikin lokutan da na yi da shi, ya fada mani cewa akwai abubuwan da zai so ya kammala amma lokaci ba zai bashi dama ba.

Kara karanta wannan

Kin jinin Musulmi: China ta yi Allah wadai da wadanda suka kona al-Qur'ani a Sweden

“Na fada masa cewa yana iya aike na ko wani daga cikin mu ya taya shi amma sai ya bayyana cewa bazan gane ba.”

Hadimin ya kuma bayyana cewa saboda yanayin sarkin, tafiyar zuwa Ado-Ekiti ya dauki dogon lokaci, rahoton PM News.

“A ranar Lahadi makon da ya gabata, mun shirya motar asibiti da yan sanda masu rakiya domin kai shi Ado-Ekiti. Akwai bukatar motar asibitin saboda kada ya kasance a zaune yayin tafiyar. Mun so ya kasance cikin walwala.
“Da ya fito daga fadar, yan uwa ne suka taimaka masa saboda jikinsa ya yi laushi. Amma da ya shiga motar daukar mara lafiya, ya janye daga wadanda ke taimaka masa wajen yin tafiya sannan ya ce zai iya shiga motar da kansa amma ya kasa duk da kokarin hawa da ya yi. Sai da aka taimaka masa ya shiga.
“Ya juya ya kalli fadar a karo na karshe.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya karyata Buhari baro-baro, ya ce an fi samun zaman lafiya a mulkin Jonathan

“Tafiya ya dauki tsawon awa biyar saboda a hankali motocin suka dunga tafiya don kada a batawa sarki rai. Kwanaki biyu bayan an isa asibitin, sai hannaye da kafafuwan da suka kumbura suka koma daidai. Ya samu sauki amma wasu lokutan, sai ya dunga kalle-kalle kamar yana kallon wani abu.
“A safiyar ranar Juma’a, ya kira matansa biyu da suka yi tafiyan tare da shi sannan ya bayyana masu cewa ya kamata su shirya su tafi gida tunda likita ya sallame shi. Bincike kan ikirarin ya nuna cewa ba gaskiya bane. Ya yi kokarin tabbatar da cewar ya ji sauki amma gaskiya yana bukatar Karin kulawa.
“Amma da yamma, sai harshensa ya karye. Duk kokari da yayi wajen magana, ba a jin sa. Sai ya daga hannayensa daga yanayin kwanciyarsa, sai ya saki sannan ya barmu.”

Sarkin Oyo ya hango mutuwarsa, ya fada mana cewa magabatansa sun yi kira - Hadimarsa

Kara karanta wannan

Sanata Ndume ya fadi wanda ya fi kowa 'dacewa; ya yi takarar Shugaban Najeriya a APC

A baya mun ji cewa wata hadima a masarautar Oyo ta yi ikirarin Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi III, ya yi hasashen mutuwarsa tun kan ta zo.

Ta bayyana hakan ne yayin da take zantawa da manema labarai a fadar sarkin Oyo a ranar Asabar, 23 ga watan Afrilu, jaridar Punch ta rahoto.

Babban basaraken kasar Yarbawan ya rasu a daren ranar Juma’a, 22 ga watan Afrilu, a asibitin koyarwa na jami’ar Afe Babalola.

Asali: Legit.ng

Online view pixel