2023: Ƙungiyar Arewa a Kano Ta Goyi Bayan Jonathan, Ta Ce Shi Zai Iya Ceto Najeriya

2023: Ƙungiyar Arewa a Kano Ta Goyi Bayan Jonathan, Ta Ce Shi Zai Iya Ceto Najeriya

  • Wata kungiya mai suna Dawo Dawo Jonathan Network ta yi kira ga al'umman Najeriya su mara wa Goodluck Jonathan baya
  • Kungiyar, ta bakin shugabanta Isa Kaskasara, a Kano ta ce Najeriya na wani mataki mai muhimmanci da ake bukatar dattijon kasa irin Jonathan
  • Kaskasara ya ce Goodluck Jonathan yana da kwarewa da dattaku da hangen nesa da ake bukata domin ceto Najeriya daga mawuyacin halin da ta shiga

Kano - Shugaban Kungiyar Dawo Dawo Network (Masu Fafutikan Ganin Jonathan ya dawo mulki) Isa Kaskasara, ya ce Fafutikan Ganin Goodluck Jonathan ya dawo mulki sadaukarwa ne ga ƙasa, rahoton The Punch.

2023: Ƙungiyar Arewa a Kano Ta Goyi Bayan Jonathan, Ta Ce Shi Zai Iya Ceto Najeriya
Zaben 2023: Ƙungiyar Arewa a Ta Goyi Bayan Jonathan, Ta Ce Shi Zai Iya Ceto Najeriya. Hoto: The Punch.

A cikin sanarwar da ya fitar a ranar Litinin a Kano, ya ce Najeriya tana kan wata muhimmiyar gaɓa, ya ƙara da cewa:

Kara karanta wannan

Kada haka ta sake faruwa: Shugaba Buhari ya kadu da jin labarin salwantar rayuka 100 a Imo

"muna bukatar mutumin kirki, wanda ya ƙware a bangarori daban-daban na tafiyar da kasar nan don ya cece mu daga halin da muke ciki."

Sanarwar mai taken, 'Dalilin da yasa ba mu da zabi da ya fi Jonathan don cigaba Najeriya', ya ce ba zai yiwu a mika Najeriya hannun yan siyasa da basu da kwarewa ba.

Politics Nigeria ta rahhoto cewa Kaskasara ya ce Jonathan ya ce dattijon ƙasa ne wanda ya bada muhimmin gudunmawa wurin inganta demokradiyya a Najeriya.

Ya cigaba da cewa a wannan lokaci mai muhimmanci, muna bukatar mutumin da ya fahimci Najeriya kuma zai iya kawo daidaito.

Mutum mai yawan magana ba zai iya shugabancin Najeriya ba, in ji Kaskasara

A cewarsa, Jonathan ya kame kansa daga sukar shugabannin baya da masu ci yanzu saboda hadin kai da gina kasa.

Kara karanta wannan

Dole ka tsaya takara: Masoya Jonathan sun mamaye ofishinsa, suna neman gafara

"Mutum mai yawan maganganu ba zai iya mulkar kasa mai mutane daban-daban irin Najeriya ba, ya kamata mu fahimci cewa mutum kamar Goodluck Ebele Jonathan ne zai iya wannan aikin.
"Mu a arewa muna tare da shi, kuma za mu tara kudi domin ganin mu dawo da shi kan mulki. Don haka muna kira ga yan Najeriya su hada kai tare da mu don gina Najeriya," in ji Kaskasara.

Yahaya Bello: Ƙaruwar Masu Fitowa Takarar Shugaban Ƙasa Baya Bani Tsoro Ko Kaɗan

A bangare guda, dan takarar shugaban kasa kuma Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce ko fargaba ba ya yi akan yadda mutane da dama suke ta fitowa takarar shugaban kasa, The Punch ta ruwaito.

Haka zalika, ya ce bai tsorata ba da shirye-shiryen yarjejeniyar jam’iyya ba saboda yana sa ran kasancewa mai nasara a ko wanne irin mataki jam’iyyar ta dauka wurin zaben dan takara.

Kara karanta wannan

Ina da kwarin guiwa da izinin Allah wannan ɗan takarar ne zai gaji Buhari a 2023, Sanatan Kano ya magantu

Ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da Kungiyar Kamfen din shugabancin kasar Yahaya Bello ta shirya a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164