Dole ka tsaya takara: Masoya Jonathan sun mamaye ofishinsa, suna neman gafara

Dole ka tsaya takara: Masoya Jonathan sun mamaye ofishinsa, suna neman gafara

  • Matasa da dattijai maza da mata sun mamaye ofishin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan
  • Sun bayyana bukatar ya sake fitowa takarar shugaban kasa, inda suka bayyana cewa lallai sun yi kuskure a baya
  • Tuni dama wata kungiyar 'yan Najeriya mazauna waje suka ba shi wa'adin ya tsaya takara a zaben na 2023

Abuja - Yayin da Najeriya ke kara kusanto da babban zaben 2023, a ranar Juma'a masu zanga-zangar sun mamaye ofishin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a Abuja, suna kira gare shi da ya ayyana tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

Jama'ar sun kunshi maza da mata da matasa, inda suka mamaye ofishin dauke da alluna da takardu na neman tsohon shugaban kasar ya shiga takarar shugaban kasa, Vanguard ta ruwaito.

Tsohon shugaba Jonathan ya shiga matsin masoya
Yanzu-Yanzu: Jama'a sun mamaye ofishin Jonathan, suna zanga-zangar ya fito takara | Hoto: vanguardngr.com

Wasu daga cikin fastocin da ke dauke da hotunan Jonathan an rubuta:

Kara karanta wannan

Abin da Shugaban kasa ya fadawa Malamai da Sarakuna da suka yi buda-baki a Aso Villa

"GoodLuck Jonathan, dole ne ka tsaya takara"

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Muna bukatar ka daidata Najeriya."

Masoyan na Jonathan sun yi imanin cewa tsohon shugaban kasar yana da tsarin da zai dawo da martabar Najeriya tare da baiwa duk ‘yan Najeriya jin dadin da suke bukata.

Jaridar Daily Trust ta nuna hotunan lokacin da jama'ar ke mamaye da ofishin na Jonathan.

Mai magana da yawun tawagar 'yan zanga-zangar, Mayor Samuel yace

“Wadanda suka ce za su iya a shekarar 2015 ne suka yaudare mu da wanke kwakwalen.
“Yanzu mun san cewa a karkashin Jonathan mafi karancin albashi na iya sayen buhunan shinkafa daya ko biyu. Me muke da shi a yau? Muna rokon Shugaba Jonathan ya gafarta mana, mun gane kura-kuranmu, muna son ya dawo ya kammala abin da ya fara."

Mazauna waje sun ba Jonathan wa'adi ya tsaya takara ko su hadu a kotu

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: NDLEA ta kai samame wurin bikin casu a Abuja, ta cafke jama'a da yawa

A jiya ne kungiyar matasan Najeriya kwararru mazauna kasashen waje (NYPD), ta baiwa Jonathan wa’adin mako guda ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 ko kuma su kai shi gaban kotu.

Kungiyar wacce ta kunshi matasa kwararru a kasashen waje ta kunshi ‘yan Najeriya daga ko’ina a cikin kasar wadanda ke aiki ko zama a kasashe daban-daban.

Babban jagoran kungoyar, Arc. Oladipo Akande a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ta sakon imel daga Los Angeles ta Amurka ya bayyana cewa ya zama dole ga tsohon shugaban kasar ya tsaya takara ba tare da bata lokaci ba.

Har yanzu ina shawarar takara, ku dakace ni: Goodluck Jonathan

A wani labarin, bayan zanga-zanga da ihun sunansa da sassafe, tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan, a ranar Juma'a ya fito don jawabi ga yan zanga-zangan da suka dira ofishinsa.

A jawabinsa, Jonathan ya bukaci matasan Najeriya sun zurfafa ra'ayinsu cikin siyasar Najeriya, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Malamin Addini: Mutane 2 ne kadai masu kyakkyawar manufa cikin masu son gaje Buhari

Tsohon shugaban kasan yace lokaci ya yi da ya kamata matasa su ci gajiyar dokar 'Not Too Young To Run Act'.

Asali: Legit.ng

Online view pixel