Na miƙa wuya Mataimakin shugaban kasa ne zai gaji Buhari a 2023, Sanatan APC daga Kano

Na miƙa wuya Mataimakin shugaban kasa ne zai gaji Buhari a 2023, Sanatan APC daga Kano

  • Sanata Kabiru Gaya mai wakiltar Kano ta kudu ya ce ba shi da tantama kan wanda zai gaji shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a 2023
  • Sanata Gaya ya bayyana cewa duba da kwarewar mataimakin shugaban ƙasa da sanin halin da ake ciki, shine zai ɗare mulkin ƙasa
  • A cewarsa da izinin Allah mai cikakken mulki da kuma ruwan kuri'un yan Najeriya, Osinbajo, zai ɗare mulki cikin sauki

Abuja - Sanata mai wakiltar Kano ta kudu, Sanata Kabiru Gaya, ya karɓi ragamar kungiyar cigaba (TPP), gamayyar kungiyoyin magoya baya masu yaɗa manufar mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo.

Da yake jawabi a wurin taron manema labarai a Abuja ranar Alhamis, Sanata Gaya, ya ce burin Osinbajo ba na ƙashin kansa bane, amsa kiran al'umma ne na tsayawa takara.

Mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo.
Na miƙa wuya Mataimakin shugaban kasa ne zai gaji Buhari a 2023, Sanatan APC daga Kano Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Sanatan ya ƙara da cewa ya na da kwarin guiwa Osinbajo ne zai gaji kujerar shugaba Buhari a zaɓen 2023, kamar yadda The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Daga ƙarshe, Jam'iyyar APC ta faɗi gaskiyar abinda ya sa ta sanya kuɗin Fom Miliyan N100m

Gaya ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ba tare da wata tantama ba, ina da yaƙinin cewa duk wasu masu hankali anan sun fahimci tare da tabbatar da nagarta da cancantar Farfesa Yemi Osinbajo."
"Ta hanyar zaɓen mutum kamar Osinbajo, wanda ya san kalubalen da muke fuskanta fiye da tunani da kuma sanin dabaru da hanyoyin magance su, muna da babbar damar cigaba cikin ƙankanin lokaci."
"Ina da kwarin guiwar cewa da karfin ikon Allah mai girma da ɗaukaka da kuma ruwan kuri'un miliyoyin yan Najeriya a faɗin sassan ƙasar nan shida, Osinbajo ne zai gaji shugaba Buhari ranar 20 ga watan Mayu, 2023."

Matasa zasu yi karo-karo su siya masa Fom

Sanatan ya bayyana cewa kungiyoyin masoya ba su da wata damuwa su tattara miliyan N100m don siyan Fom ɗin sha'awar takara na jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Mutanen dake ɗaukar nauyin yan bindiga a jihata, Gwamnan APC ya fasa kwai

"Tawagar matasa tare da TPP sun ce zasu tattara miliyan N100m ta hanyar kowane mamba ɗaya ya ba da N10,000 cikin masoya 10,000 da suka shirya ganin goben su ta yi kyau."

A wani labarin kuma Na hannun daman gwamna Ganduje ya canza shawara, ya janye daga takarar gwamna a 2023

Sakataren gwamnatin jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji, ya janye daga tseren takarar gwamnan jihar a zaɓe mai zuwa.

Bayanai sun nuna cewa Alhaji ya ɗauki wannan matakin ne biyo bayan gana wa da mai girma gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel