Osinbajo, Tambuwal da sauran 'yan takarar shugaban kasa 10 da basu halarci taron Iftar din Aisha Buhari ba

Osinbajo, Tambuwal da sauran 'yan takarar shugaban kasa 10 da basu halarci taron Iftar din Aisha Buhari ba

A ranar Asabar, 23 ga watan Afrilu, ne uwargidar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha ta gayyaci yan takarar shugaban kasa a fadin jam’iyyun siyasa zuwa taron buda baki.

Yayin da wasu yan takarar shugaban kasa daga jam’iyyun All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP) suka amsa gayyatar, wasu basu halarci liyafar cin abincin daren ba.

Osinbajo, Tambuwal da sauran 'yan takarar shugaban kasa 10 da basu halarci taron Iftar din Aisha Buhari ba
Osinbajo, Tambuwal da sauran 'yan takarar shugaban kasa 10 da basu halarci taron Iftar din Aisha Buhari ba Hoto: Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Ga jerin manyan yan takarar shugaban kasa da basu halarci liyafar ba:

1. Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo (APC, ya samu wakilcin tsohon gwamnan jihar Edo, Farfesa Oserheimen Osunbor)

2. Ministan sufuri Rotimi Amaechi (APC)

3. Sanata Rochas Okorocha (APC)

4. Tsohon mataimakin shugaban Atiku Abubakar (PDP)

Kara karanta wannan

Hotuna: Tinubu, 'yan takarar PDP da wasu kusoshi sun halarci Iftar din Aisha Buhari

5. Tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki (PDP)

6. Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas (PDP)

7. Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto (PDP)

8. Gwamna Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom (PDP)

9. Tsohon gwamnan Ekiti Ayo Fayose (PDP)

10. Tsohon gwamnan Anambra Peter Obi (PDP)

11. Dele Momodu (PDP)

12. Sanata Anyim Pius Anyim (PDP)

Aisha Buhari na so mata su zama abokan takarar masu neman kujerun shugabanci a 2023

A gefe guda, uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari, ta bukaci jam’iyyun siyasa da su dunga duba yiwuwar tsayar da mata a matsayin abokan takarar masu neman kujerun shugabanci a zaben kasar.

Aisha ta bayyana hakan ne yayin da take jawabi a daren ranar Asabar, 23 ga watan Afrilu, lokacin da ta karbi bakuncin masu neman takarar shugaban kasa daga jam’iyyu daban-daban a wajen buda baki a fadar shugaban kasa, Abuja, jaridar The Guardian ta rahoto.

Kara karanta wannan

Jerin sunayen manyan yan siyasa 5 da suka sauya sheka daga APC zuwa PDP a kwanan nan

Uwargidar shugaban kasar ta shirya taron buda bakin ne domin ba masu neman takarar damar wanzar da soyayya da farin ciki a tsakaninsu a cikin wannan wata ta Ramada da kuma kokarin hada kan kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel