Hotuna: Tinubu, 'yan takarar PDP da wasu kusoshi sun halarci Iftar din Aisha Buhari

Hotuna: Tinubu, 'yan takarar PDP da wasu kusoshi sun halarci Iftar din Aisha Buhari

  • Wasu 'yan takarar shugabancin kasa na jam'iyyun PDP da APC duk sun halarci taron buda-baki da Aisha Buhari ta shirya a Aso Villa
  • Wurin karfe 6:20, an ga Bola Tinubu, Gwamna Bala Mohammed, Gwamna Dave Umahi amma babu Atiku Abubakar
  • Wasu jiga-jigan 'yan siyasa a kasar nan da kusoshi irinus ministan kwadago, Chris Ngige da ministan Niger-Delta, Godswill Akpabio sun hallara

FCT, Abuja - Wasu daga cikin 'yan takarar shugabancin kasa da masu mukaman siyasa da ke dukkan jam'iyyun siyasar kasar nan a halin yanzu sun hallara liyafar buda-bakin da uwargidan shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari ta shirya a tsohon dakin taro na Banquet da ke fadar shugaban kasa a Abuja.

Daily Trust ta ruwaito cewa, daga cikin 'yan takarar shugabancin kasar da suka halarta a yayin rubuta wannan rahoton, akwai jigon jam'iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu, Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi da gwamnan Bauchi, Gwamna Bala Mohammed na jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Zaɓen 2023: Kada Ka Ruɗa Ƴan Najeriya, Ƙungiya Ta Ja Kunnen Atiku

Da duminsa: Tinubu, 'yan takarar PDP da wasu kusoshi sun halarci Iftar din Aisha Buhari
Da duminsa: Tinubu, 'yan takarar PDP da wasu kusoshi sun halarci Iftar din Aisha Buhari. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sauran jiga-jigan da suka halarci taron wurin karfe 6:20 na yammaci, akwai Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, ministan kwadago da aikin yi, Sanata Chris Ngige, ministan al'amuran Niger Delta, Godswill Akpabio, tsohon shugaban PDP Branabas Gemade, tsohon kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara da kuma fitaccen dan kasuwar mai, Tein Jack-Rich.

The Nation ta ruwaito cewa, uwargidan shugaban kasan ta gayyaci dukkan 'yan takarar shugabancin kasa daga dukkan jam'iyyun siyasar kasar nan zuwa taron buda-baki da za a yi da karfe 6:30 na yammcin Asabar.

Da duminsa: Tinubu, 'yan takarar PDP da wasu kusoshi sun halarci Iftar din Aisha Buhari
Da duminsa: Tinubu, 'yan takarar PDP da wasu kusoshi sun halarci Iftar din Aisha Buhari. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Da duminsa: Tinubu, 'yan takarar PDP da wasu kusoshi sun halarci Iftar din Aisha Buhari
Da duminsa: Tinubu, 'yan takarar PDP da wasu kusoshi sun halarci Iftar din Aisha Buhari. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Kada kowa yazo da waya: Aisha Buhari ta shirya liyafa ga 'yan takarar shugaban kasa a dukkan jam'iyyu

A wani labari na daban, uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari, ta gayyaci dukkanin yan takarar shugaban kasa daga jam’iyyun siyasa zuwa taron buda bakin Ramadana a fadar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Da duminsa: An yi Sallar Jana'izar Alaafin Oba Lamidi Adeyemi

Za a gudanar da taron shan ruwan ne a dakin taro na gidan gwamnati a ranar Asabar, 23 ga watan Afrilu, da misalin karfe 06:30 na yamma.

A wasikar gayyatan, an umurci yan takarar da kada su zo da wayarsu sai katin gayyatar kawai wanda shine zai basu damar shiga fadar shugaban kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel