Jerin sunayen manyan yan siyasa 5 da suka sauya sheka daga APC zuwa PDP a kwanan nan

Jerin sunayen manyan yan siyasa 5 da suka sauya sheka daga APC zuwa PDP a kwanan nan

Gabannin babban zaben 2023, manyan yan siyasa a jam’iyyun All Progressives Congress (APC) mai mulki da Peoples Democratic Party (PDP) mai adawa sun fara sauye-sauyen sheka domin kare kudirin siyasarsu.

A yan kwanakin nan da suka gabata, jam’iyyar APC mai mulki ta rasa wasu manyan mambobinta zuwa PDP.

Ga manyan jiga-jigan APC da suka koma PDP gabannin babban zaben kasar mai zuwa.

Jerin sunayen manyan yan siyasa 5 da suka sauya sheka daga APC zuwa PDP a kwanan nan
Jerin sunayen manyan yan siyasa 5 da suka sauya sheka daga APC zuwa PDP a kwanan nan Hoto: @reportdailys, @Team_Tegbe, @coretvnewsng, @nigeriantribune
Asali: UGC

1. Ahmed Babba Kaita

Ahmed Babba Kaita, sanata mai wakiltan Katsina ta arewa, yankin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sauya sheka daga APC zuwa PDP a ranar Laraba, 20 ga watan Afrilu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wata sanarwa daga hadimin labaransa, Abdulkadir Lawal, Babba-Kaita ya ce ya sauya sheka ne saboda yadda gwamnan jihar, Bello Masari ya yi babakere ya hana ruwa gudu a harkar jam’iyyar a jihar.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Kotu ta kori tsohon kakakin majalisa Dogara daga majalisar wakilai

Ya kuma bayyana cewa PDP na wakiltan ra’ayinsa.

2. Mogaji Joseph Tegbe

Hakazalika, tsohon dan takarar gwamna karkashin APC a jihar Oyo, Mogaji Joseph Tegbe, ya sauya sheka zuwa PDP.

Hakan ya faru ne saboda yawan rikice-rikice a APC wanda ya ki ci ya ki cinyewa.

An sanar da batun sauya shekar Tegbe ne a daren ranar Talata, 12 ga watan Afrilu, ban tsawon wwatanni yana fuskantar matsin lamba.

3. Aminu Muhammad Achida

Kakakin majalisar dokokin jihar Sokoto, Aminu Muhammad Achida, ya bar APC zuwa PDP.

Achida ya gabatar da wasikar sauya sheka ga majalisar dokokin a lokacin zamanta na ranar Alhamis, 14 ga watan Afrilu.

4. Murtala Bello Maigona Murtala

Bello Maigona, dan majalisar dokokin jihar Sokoto mai wakiltan mazabar Wammako 2, ya zama dan PDP a yanzu.

An sanar da sauya shekarsa daga APC tare da na kakakin majalisar, Achida.

5. Abubakar Sulaiman

Kara karanta wannan

PDP ta ci kasuwa da kudin saida fam, ta tashi da N600m daga hannun ‘Yan takara 17

Kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi, Rt. Hon. Abubakar Sulaiman ma ya koma PDP.

An zabe shi a matsayin dan majalisa mai wakiltan mazabar Ningi a 2019 a karkashin inuwar jam’iyyar APC.

Sulaiman wanda ya kuma kasance shugaban kungiyar yan majalisun jiha na Najeriya, ya sanar da batun sauya shekarsa a lokacin buda bakin Ramadana wanda Gwamna Bala Mohammed ya shirya, wanda aka yi a gidan gwamnatin jihar Bauchi a daren Asabar, 16 ga watan Afrilu.

Katsina: Sakataren Gwamnati, Mustapha Inuwa ya yi murabus daga kan muƙaminsa

A wani labarin, sakataren gwamnatin jihar Katsina, Mustapha Muhammad Inuwa, ya yi murabus daga kan muƙaminsa a yunkurin da yake na gaje kujerar gwamna Aminu Bello Masari.

Inuwa, wanda ya jima da ayyana shiga tseren takarar gwamnan Katsina a 2023 ƙarƙashin APC, mafi yawan mutane na ganin babban ƙusa ne kuma zai iya lallasa sauran yan takara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel