Aisha Buhari na so mata su zama abokan takarar masu neman kujerun shugabanci a 2023

Aisha Buhari na so mata su zama abokan takarar masu neman kujerun shugabanci a 2023

  • Aisha Buhari ta nemi jam'iyyun siyasa su tsayar da mata a matsayin abokan takarar masu neman mukaman shugabanci a 2023
  • Uwargidar shugaban kasar ta ce yin hakan shine zai zamo adalci ga mata duba ga karfin kuri'unsu da rawar ganin da suke takawa a yayin zabe
  • Ta kuma yi kira ga masu neman shugabancin kasar da su nuna juriya, adalci da hana tashin hankali tare da hada kan kasar musamman a yakin neman zabe

Abuja - Uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari, ta bukaci jam’iyyun siyasa da su dunga duba yiwuwar tsayar da mata a matsayin abokan takarar masu neman kujerun shugabanci a zaben kasar.

Aisha ta bayyana hakan ne yayin da take jawabi a daren ranar Asabar, 23 ga watan Afrilu, lokacin da ta karbi bakuncin masu neman takarar shugaban kasa daga jam’iyyu daban-daban a wajen buda baki a fadar shugaban kasa, Abuja, jaridar The Guardian ta rahoto.

Kara karanta wannan

Jerin yan takarar shugaban kasa 5 da suka ce Ubangiji ne ya kira su domin yin takara

Uwargidar shugaban kasar ta shirya taron buda bakin ne domin ba masu neman takarar damar wanzar da soyayya da farin ciki a tsakaninsu a cikin wannan wata ta Ramada da kuma kokarin hada kan kasa.

Aisha Buhari na so mata su zama abokan takarar masu neman kujerun shugabanci a 2023
Aisha Buhari na so mata su zama abokan takarar masu neman kujerun shugabanci a 2023 Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ta ce, yin adalci ga mata a harkokin siyasa shi ne tabbatar da ganin cewa sun shiga an dama da su a mukaman shugabanci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta ce:

“A zahirin gaskiya, lokaci ya yi da za a tsayar da mata a matsayin abokan takara a dukkan matakai duba ga karfin kuri’unsu da kuma yadda suke taka rawa a tsare-tsaren siyasa.
“Yayin da muke tunkarar zaben 2023 da kyakkyawan fata, ina da yakinin cewa Najeriya za ta ci gaba da habbaka daga karfi zuwa karfi a kan turbar dimokuradiyyarmu."

Uwargidan shugaban kasar, ta bukaci masu neman shugabancin kasar da su ci gaba da mai da hankali kan batutuwan da za su karfafa hadin kan al'ummar kasar, 'yan uwantaka da hadin kan kasa.

Kara karanta wannan

Ku yi koyi da Dangote: Buhari ya ba 'yan kasuwan Najeriya shawari mai ban mamaki

Sai dai Aisha ta tunatar da bakinta cewa, zaben 2015 ya kafu a tarihin Najeriya.

“Ba a yi takara ba a kotun shari’a, ko kuma a kotun ra’ayin jama’a.
“Don haka babban tukwicin kammala wa’adin mulki da yan Najeriya za su baiwa iyalan shugaban kasar shine wani zabe na gaskiya da amana a 2023."

Ta bukaci dukkanin yan takara da su zamo masu juriya, yin adalci tare da kaucewa tashin hankali ta hanyar dinke baraka a inda ya dace, musamman a lokacin yakin neman zabe, rahoton Premium Times.

Tinubu, 'yan takarar PDP da wasu kusoshi sun halarci Iftar din Aisha Buhari

A baya mun ji cewa wasu daga cikin 'yan takarar shugabancin kasa da masu mukaman siyasa da ke dukkan jam'iyyun siyasar kasar nan a halin yanzu sun hallara liyafar buda-bakin da uwargidan shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari ta shirya a tsohon dakin taro na Banquet da ke fadar shugaban kasa a Abuja.

Kara karanta wannan

2023: Kwana Kaɗan Bayan Buhari Ya Musu Afuwa, An Yi Kira Ga Dariye Da Nyame Su Fito Takarar Shugaban Ƙasa

Daily Trust ta ruwaito cewa, daga cikin 'yan takarar shugabancin kasar da suka halarta a yayin rubuta wannan rahoton, akwai jigon jam'iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu, Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi da gwamnan Bauchi, Gwamna Bala Mohammed na jam'iyyar PDP.

Sauran jiga-jigan da suka halarci taron wurin karfe 6:20 na yammaci, akwai Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, ministan kwadago da aikin yi, Sanata Chris Ngige, ministan al'amuran Niger Delta, Godswill Akpabio, tsohon shugaban PDP Branabas Gemade, tsohon kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara da kuma fitaccen dan kasuwar mai, Tein Jack-Rich.

Asali: Legit.ng

Online view pixel