Da dumi-dumi: Kotu ta kori tsohon kakakin majalisa Dogara daga majalisar wakilai

Da dumi-dumi: Kotu ta kori tsohon kakakin majalisa Dogara daga majalisar wakilai

  • Sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC ta ja wa tsohon kakakin majalisar wakilai rasa kujerarsa
  • A yau ne kotu ta ce ta kori Yakubu Dogara daga kujerar dan majalisar wakilai, kana za a nemo mai maye gurbinsa
  • Wannan dai ya yi daidai da tsarin doka, kamar yadda wani masanin doka ya shaidawa wakilinmu

Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta kori Yakubu Dogara daga mukaminsa na dan majalisar wakilai tare da bayyana neman mai maye kujerarsa.

Dogara, wanda ke wakiltar mazabar Bogoro/Dass a jihar Bauchi, ya kasance kakakin majalisar wakilai ta tarayya tsakanin 2015 zuwa 2019, inji rahoton Premium Times.

Kotu ta kwace kujerar Yakubu Dogara
Da dumi-dumi: Kotu ta kori tsohon kakakin majalisa Dogara daga majalisar wakilai | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Alkalin kotun, D.U. Okorowo, a ranar Juma’a, ya yanke hukuncin cewa ficewar Dogara daga jam’iyyar PDP jam’iyyar APC kuskure ne kuma hakan na nufin ya bar kujerarsa ta majalisa.

Kara karanta wannan

2023: Shehu Sani ya hango yadda APC da PDP za su zabi 'yan takarar shugaban kasa

Da yake yanke hukunci, ya bayyana cewa bayan sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC, Dogara bai cancanci ci gaba da zama kan kujerarsa ba daidai da sashe na 68(1)(g) na kundin tsarin mulki, inji rahoton Punch.

Dogara dai ya koma APC ne bayan ya sake lashe zabe a karkashin jam’iyyar PDP a zaben 2019 da ya gabata.

Rashin jituwarsa da gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, na daya daga cikin manyan dalilan da ya sa ya fice daga jam'iyyar PDP da ya shiga kasa da shekaru biyar da suka wuce.

Ficewar Dogara daga PDP

Dogara a ranar 24 ga Yuli, 2020 ya fice daga PDP ya koma tsohuwar jam’iyyarsa ta APC.

A farkon shekarar 2018 ne Dogara ya fice daga jam’iyya mai mulki zuwa babbar jam’iyyar adawa bayan ya shafe kusan shekaru biyu suna adawa da gwamnan jihar Bauchi a lokacin Mohammed Abubakar.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Har yanzu ina shawarar takara, ku dakace ni: Goodluck Jonathan

Masanin doka a babban birnin tarayya Abuja, Isa Usman Esq. ya shaidawa wakilin Legit.ng Hausa cewa:

"Wannan ba sabon abu bane, amma watakila ya daukaka kara, domin mun sha ganin hakan. Amma dai doka ce ta kasa ta tanadi hakan kuma tabbas ya kamata sun sani.
"Yana iya daukaka karar yanzu saboda ya yi jinkiri har wa'adin mulkin ya kare, to amma abin tambaya anan shi ne; meye makomar siyasarsa ta gaba idan yana son tsayawa takara a zaben 2023? Wannan ne ba zan iya cewa komai ba."

Bayan ya koma APC, ‘Ya ‘yan Jam’iyya sun fara rigima da Yakubu Dogara a jihar Bauchi

A wani labarin, wasu ‘yan jam’iyyar APC da aka bata wa rai a reshen karamar hukumar Tafawa-Balewa, da ke jihar Bauchi, suna kuka da Rt. Hon. Yakubu Dogara.

Jaridar Punch ta kawo labari cewa ‘ya ‘yan jam’iyyar suna zargin tsohon shugaban majalisar wakilan da yin karfa-karfa a zaben shugabanni da za ayi.

Kara karanta wannan

Komin rashin tsaro sai mun yi zaben 2023, Shugaban hukumar INEC

Kamar yadda rahoton ya bayyana, ana zargin Rt. Hon. Yakubu Dogara ya karbe fam din shiga takarar zaben shugabannin APC na kananan hukumomi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel