Komin rashin tsaro sai mun yi zaben 2023, Shugaban hukumar INEC

Komin rashin tsaro sai mun yi zaben 2023, Shugaban hukumar INEC

  • Komin rashin tsaro zamu yi iyakan kokari wajen ganin mun gudanar da zaben 2023, Shugaban hukumar INEC
  • Farfesa Yakubu ya yi kira ga yan Najeriya su baiwa hukumar goyon baya wajen samun nasarar gudanar da zaben 2023
  • Hukumar INEC ta ware kimanin naira bilyan 240 don gudanar da zaben 2023

Abuja - Hukumar shirya zabukan kasa INEC a ranar Alhamis ta bayyana cewa za'ayi zaben 2023 duk da matsalar tsaron da kasar ke ciki.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu, ya bayyana hakan a Abuja yayin gabatar da takardar shirin da hukumar ta yiwa zaben 2023, rahoton Channels Tv.

Yace:

"Muna sane da matsalolin tsaro da tasirin da hakan ke iya wa zabe. Zamu cigaba da hada kai da jami'an tsaro domin tabbatar tsaron ma'aikata da kayayyakinmu, masu lura, yan jarida, da masu zabe."

Kara karanta wannan

Kashe-kashen Kanam: Yadda gwamna Lalong ya yi watsi da gargadin da nayi masa – Shugaban karamar hukuma

"Tabbas akwai kalubale amma muna kan bakanmu sai an yi zabe a 2023."

Farfesa Yakubu ya yi kira ga yan Najeriya su baiwa hukumar goyon baya wajen samun nasarar gudanar da zaben 2023.

Komin rashin tsaro sai mun yi zaben 2023, Shugaban hukumar INEC
Komin rashin tsaro sai mun yi zaben 2023, Shugaban hukumar INEC
Asali: Facebook

INEC ta karyata Tinubu a karo na 2 a wata 1, ta yi wa jigon APC martani kan batun katin zabe

A wani labarin kuwa, Shugaban hukumar zabe mai zaman kan ta, Farfesa Mahmood Yakubu ya yi karin haske a game da wani jita-jita da ke ta faman yawo a kasar nan.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Farfesa Mahmood Yakubu yana musanya ikirarin cewa katin kada kuri’a watau PVC ya kan tashi daga aiki idan har ya dade.

Da yake jawabi a garin Abuja a ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu 2022, shugaban hukumar zaben na kasa ya ce katin ba su da ranar daina aiki a Najeriya.

Kara karanta wannan

Ba Za Ku Iya Maguɗin Zaɓe Ba a 2023, Buhari Ya Faɗa Wa 'Yan Siyasa

Mahmood Yakubu ya ba masu zabe tabbacin cewa za'a yi amfani da PVC a wajen kowane zabe.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel