An samu ‘Yan siyasa 2 da suka saye fam a PDP, za su jarraba sa’a kan Zulum a 2023

An samu ‘Yan siyasa 2 da suka saye fam a PDP, za su jarraba sa’a kan Zulum a 2023

  • PDP ta samu Naira miliyan 42 daga hannun Alhaji Muhammed Imam da Muhammed Ali a jihar Borno
  • Wadannan ‘yan siyasa biyu sun saye fam da nufin neman takarar Gwamnan Borno a Jam’iyyar
  • Babu mamaki duk wanda ya yi nasara a cikinsu ya yi takara da Babagana Umara Zulum a zaben 2023

Borno - Wasu jiga-jigai a jam’iyyar hamayya ta PDP sun yanki fam din shiga takarar gwamna a jihar Borno, da nufin yin takara a zabe mai zuwa.

Kamar yadda Daily Trust ta kawo rahoto a ranar Alhamis, 21 ga watan Afrilu 2022, wadannan ‘yan siyasa za su nemi su kifar da gwamnatin APC mai-ci.

Muhammed Imam da Muhammed Ali sun biya N21m, sun mallaki fam din takarar kujerar gwamnan jihar Borno a jam’iyyar PDP a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya fadi wanda za a fifita a tsarin da aka dauko na fito da ‘Dan takarar 2023

Rahoton ya ce wadannan ‘yan siyasa sun kammala cike fam din, kuma sun dawo da shi ga jam’iyya, su na sauraron ranar zaben fitar da gwani.

Hakan na zuwa ne bayan an yi ta yada labarai cewa an rasa wani ‘dan siyasa da zai kalubalanci Farfesa Babagana Umara Zulum wanda yake kan mulki.

Bisa dukkan alamu Farfesa Babagana Umara Zulum zai nemi tazarce a 2023, shi ma ana yawan jita-jitar zai yi takarar mataimakin shugaban Najeriya.

Gwamnan Borno
Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum Hoto: @GovBorno
Asali: Twitter

A 2019, Imam ya yi wa PDP takara a Borno, ya samu kuri’a 66, 000 yayin da APC ta samu miliyan 1.17.

Da kamar wahala?

Legit.ng Hausa ta na da labari cewa jam’iyyar PDP ba ta taba yin mulki a jihohin Borno da Yobe ba tun da aka dawo mulkin farar hula a Mayun 1999.

Kara karanta wannan

PDP ta ci kasuwa da kudin saida fam, ta tashi da N600m daga hannun ‘Yan takara 17

Abubakar Mala Kachalla ne ya zama gwamna a 1999 a karkashin APP. Amma Marigayin bai iya samun tikitin tazarce a jam’iyyar ANPP a 2023 ba.

Hakan ta sa dole Kachalla ya sauya-sheka zuwa jam’iyyar AD, ya sha kasa a zaben gwamna a hannun Ali Modu Sheriff wanda shi ya tsaya a ANPP.

A irin haka Kashim Shettima ya zama gwamna a 2011, ya kuma yi shekaru takwas a mulki. Babagana Zulum ne ya zama magajinsa da zai tafi a 2019.

A halin yanzu Gwamna Zulum yana cikin ‘yan siyasa masu farin jini sosai a kasar nan. Hakan ta sa ake ganin sai PDP tayi da gaske za ta iya kai labari.

Ndume na tare da Amaechi

Yayin da Kashim Shettima ke tare da Bola Tinubu, sai aka ji labari Sanata Muhammad Ali Ndume ya na goyon bayan Rotimi Amaechi ya zama shugaban kasa.

'Dan majalisar na kudancin jihar Borno ya ce Ministan ya fi Bola Tinubu da Farfesa Yemi Osinbajo cancanta da tikitin APC, don haka ne yake mara masa baya.

Kara karanta wannan

Jagororin APC 20 da suka sa baki aka yi wa ‘Yan kasa da shekara 40 rangwamen fam

Asali: Legit.ng

Online view pixel