PDP ta ci kasuwa da kudin saida fam, ta tashi da N600m daga hannun ‘Yan takara 17

PDP ta ci kasuwa da kudin saida fam, ta tashi da N600m daga hannun ‘Yan takara 17

  • Kawo yanzu an rufe saida fam din shiga takarar kujerar siyasa a zabe mai zuwa a jam’iyyar PDP
  • Maza 16 da ke neman takarar shugaban Najeriya a jam’iyyar PDP sun kashe N640m a sayen fam
  • An yi wa matasa da mata rangwame, don haka Oliver Tareila Diana ta biya Naira miliyan shida kacal

Abuja - Jam’iyyar hamayya ta PDP ta kammala saida fam ga masu sha’awar tsayawa takarar siyasa a zaben 2023. Daily Trust ta fitar da wannan rahoto.

Ana kyautata zaton akalla mutane 17 suka saye fam din shiga takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP. Da su ne za a kara wajen zaben fitar da gwani.

Jaridar ta bibiyi wadanda suka saye fam na neman shugaban kasa a PDP, ta ce da kudin fam din, babbar jam’iyyar adawar ta samu kimanin Naira miliyan 646.

Kara karanta wannan

An samu ‘Yan siyasa 2 da suka saye fam a PDP, za su jarraba sa’a kan Zulum a 2023

Daga cikin wadanda suka lale kudi suka saye fam a PDP akwai tsohon mataimakin shugaban kasa kuma ‘dan takarar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar.

Akwai tsofaffin shugabannin majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki da Anyim Pius Anyim. Sai kuma Peter Obi wanda yake tare da Atiku Abubakar a 2019.

Akwai gwamnonin jihohin Sokoto, Bauchi, Abia da na Ribas; Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal, Bala Mohammed, Udom Emmanuel da kuma Nyesom Wike.

'Ya 'yan PDP
'Yan takarar PDP tare da Ifeanyi Ugwuanyi Hoto: @bukolasaraki Daga: Twitter
Asali: Twitter

Hayatu-Deen, Ndukwe, da Kalu sun saye fam

PDP ta samu kudi da masanin tattalin arziki kuma tsohon ma'aikacin banki, Mohammed Hayatu-Deen da kwararren malamin kwayoyi, Mazi Sam Ohuabunwa.

Tsohon shugaban majalisar Abia, Cosmos Ndukwe, Charles Ugwu, da Rt Hon Chikwendu Kalu su na cikin wadanda suke neman takarar shugaban kasa a PDP.

Kara karanta wannan

Jagororin APC 20 da suka sa baki aka yi wa ‘Yan kasa da shekara 40 rangwamen fam

Oliver Tareila Diana ta biya N6m

Sauran sun hada da wani kwararren likita a kasar waje Nwachukwu Anakwenze da Dele Momodu. Sai Ayo Fayose da mace daya, Oliver Tareila Diana.

Oliver Tareila Diana ce kurum wanda ta biya N6m domin sayen fam din saboda ita mace ce. Wasu daga cikin ‘yan takarar ba da kudinsu aka biya N40m din ba.

Nan da 28 zuwa 29 ga watan Mayun 2022 kowa zai san matsayinsa. A wannan lokaci shugabannin jam’iyyar za su shirya zaben fito da ‘dan takara.

APC ta ragewa matasa kudin fam

A jiya aka ji shugaban matasan APC na kasa ya bada sanarwar cewa za ayi wa duk wani matashi rangwame wajen sayen fam din shiga takara a jam’iyyar.

Kamar yadda Dayo Israel ya fada, duk wanda bai kai shekara 40 ba, zai saye fam din ne a rabin farashin da za a saidawa sauran masu neman shiga takara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel