Jigon APC ya fadi wanda za a fifita a tsarin da aka dauko na fito da ‘Dan takarar 2023

Jigon APC ya fadi wanda za a fifita a tsarin da aka dauko na fito da ‘Dan takarar 2023

  • Tsarin da jam’iyyar APC ta dauka na fito da ‘Dan takarar Shugaban Najeriya zai fi fifita Bola Tinubu
  • Joe Igbokwe ya ji dadin ganin matsayar da shugabanni APC suka dauka a taron majalisar NEC na jiya
  • Hadimin gwamnan jihar Legas yana ganin Ubangidansa yana da mutanen da za su iya kai ga nasara

Lagos - Daya daga cikin jagororin tafiyar jam’iyyar APC a jihar Legas, Joe Igbokwe, ya yi magana a kan matsayar da aka dauka wajen zaben majalisar NEC.

Joe Igbokwe ya yi hira da jaridar Punch, inda ya tabo batun tsarin da shugabannin jam’iyyar APC suka zaba a wajen fito da ‘dan takararsu na shugaban kasa.

A zaman NEC na farko da shugaban jam’iyya, Sanata Abdullahi Adamu ya jagoranta, an amince da cewa manyan ‘yan jam’iyya ne za su tsaida ‘yan takara.

Kara karanta wannan

An samu ‘Yan siyasa 2 da suka saye fam a PDP, za su jarraba sa’a kan Zulum a 2023

A maimakon ayi zaben ‘yar tinke ko kato-bayan-kato inda kowane ‘dan jam’iyya zai kada kuri’a, majalisar kolin APC za ta zabi wasu ne kurum su yi zaben.

Joe Igbokwe wanda ‘dan a-mutun Bola Ahmed Tinubu ne, ya shaidawa ‘yan jarida cewa mai gidansu zai doke kowa wajen samun tikitin jam’iyyar APC.

Abin da ya sa Tinubu zai kai labari

A cewar Joe Igbokwe, Bola Tinubu yana da magoya baya a cikin jam’iyya, don haka zai yi nasara muddin ba maslaha aka yi amfani wajen bada tuta a APC ba.

Jiga-jigan APC
Taron APC NEC Hoto: @OfficialAPCNig
Asali: Facebook

“Wannan tsari a bude yake, za a je filin zabe, sai ‘yan delegates su yi zabe. Bari mu jira mu gani, Asiwaju (Tinubu) zai doke su.”
“Idan da an zabi dayar hanyar (a nemi ayi maslaha tsakanin masu takara), da zai kasance fadar shugaban kasa ta saye kowa.”

Kara karanta wannan

Buhari ga shugabannin APC: Ku haramtawa PDP mulki a 2023 kamar yadda kuka yi a 2015

“Wannan tsari ya fi taimakon Asiwaju, zai yi maganin wadanda suke sauraron masu neman shugaban kasa, su ba su kudi.”
“Tsarin zai yi fatali da mashiriritan mutane, ko ma dai ya abin ya kasance, Asiwaju (Tinubu) yana da tulin mutane a kasa.”

- Joe Igbokwe

Osinbajo ba su kai labari ba

Hadimin na gwamna Babajide Sanwo-Olu yana sa ran Tinubu zai yi galaba a kan Yemi Osinbajo; Rotimi Amaechi; Chris Ngige; da sauran masu neman tikitin.

Duk wanda ya yi nasara a zaben fitar da gwani, zai gwabza da PDP da sauran jam'iyyun hamayya.

Matasa sun samu rangwame

Dayo Israel ya ce shugaba Muhammadu Buhari, Yemi Osinbajo, da Ahmad Lawan, sun taka rawar gwani wajen yi wa ‘yan kasa da shekara 40 rangwamen fam.

Haka nan kuma Gwamnonin jihohi sama da 10 sun goyi bayan rage kudin sayen fam ga matasan da suke neman takara a zaben 2023 a karkashin jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Jam’iyyar ADP ta hade da wasu jam’iyyu 16 domin fatattakar APC daga Villa

Asali: Legit.ng

Online view pixel