Ana wata ga wata: Jam’iyyar ADP ta hade da wasu jam’iyyu 16 domin fatattakar APC daga Villa

Ana wata ga wata: Jam’iyyar ADP ta hade da wasu jam’iyyu 16 domin fatattakar APC daga Villa

  • Jam'iyyar Action Democratic Party (ADP) na shirin yin maja da wasu jam'iyyu 16 gabannin zaben 2023
  • Hakan na daga cikin kokarin jam'iyyar na son ganin ta fatattaki jam'iyyar APC mai mulki daga kan kujerar shugaban kasa
  • Sai dai jam'iyyar ta bayyana cewa suna kokarin ganin sun fito da yan takara da suka cancanta a babban zaben kasar mai zuwa

Abia - Gabannin zaben 2023, jam’iyyar Action Democratic Party (ADP) ta kulla yarjejeniya da wasu jam’iyyu 16 a kasar domin su hade su zama daya.

Shugaban ADP a jihar Abia kuma ma’ajin jam’iyyar na kasa, Okey Udoh ne ya bayyana hakan, jaridar Punch ta rahoto.

Da yake zantawa da manema labarai a Umuahia, Udoh ya bayyana cewa jam’iyyar na tattaunawa domin kulla yarjejeniya mai suna ‘Third Force’ tare da wasu jam’iyyu 16.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa 'yan APC ke kara yawan mabiya a Najeriya, inji ministan Buhari

Ana wata ga wata: Jam’iyyar ADP ta hade da wasu jam’iyyu 16 domin fatattakar APC daga Villa
Ana wata ga wata: Jam’iyyar ADP ta hade da wasu jam’iyyu 16 domin fatattakar APC daga Villa Hoto: Punch
Asali: UGC

A cewarsa, ADP na daya daga cikin manyan jam’iyyu masu karfi a kasar tun daga 2019.

Udoh ya ce:

“Jam’iyyar na kokarin yin maja da zai samar da yan takara mafi cancanta amma koma me ya faru, APC ba za ta rasa sunanta ba.”

Ya kara da cewa:

“ADP za ta iya cin gashin kanta kuma sauran da za su iya zuwa su yi maja ba za su iya hadiye ta ba. Wannan hadewa da za su yi ba zai kashe sunan ADP ba.”

Ya kuma bayyana cewa da hadin gwiwar gwamnonin jiha, ADP na kokarin gina cibiyar bincike kan damokradiyyar Afrika da zai ba masu bincike damar sanin karin abubuwa game da damokradiyyar Afrika.

A tarukanta, Udoh ya ce jam’iyyar ta yi tarukanta na jiha da kananan hukumomi yana mai bayyana cewa zuwa Yuli, jam’iyyar za ta duba yiwuwar yin zabe na bai daya don gujewa matsaloli.

Kara karanta wannan

Shugaban masu rinjaye a majalisar Bauchi ya karyata rade-radin barinsa APC zuwa PDP

Bidiyon yadda Ganduje ya kalli Wike ido cikin ido ya fada masa cewa ba zai kai labari ba a 2023

A wani labari na daban, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya kalli takwaransa na jihar Ribas, Nyesom Wike a cikin ido sannan ya sanar masa da cewa ba zai yi nasara ba a kokarinsa na son gaje shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2023.

Ganduje ya yi sakin zancen ne a lokacin da Wike ya ziyarci jiharsa a yayin da yake ci gaba da tuntubar al’umman yankin arewacin Najeriya domin samun goyon bayansu.

Sai dai kuma cike da barkwanci, Gwamna Ganduje ya ce Wike na birge shi saboda kasancewarsa daga cikin mutane masu karfin gwiwa, wanda koda sun fadi a yau za su sake tashi domin sake gwada sa’arsu a gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel