Yanzu-yanzu: Tsaffin Gwamnoni da Gwamnoni masu ci ke raba kan 'ya'yan jam'iyya, Abdullahi Adamu

Yanzu-yanzu: Tsaffin Gwamnoni da Gwamnoni masu ci ke raba kan 'ya'yan jam'iyya, Abdullahi Adamu

  • Taron majalisar zartaswar jam'iyya mai gwamnati, APC, ya dau zafi yayinda shugaban ya fara caccakan gwamnoni
  • Sanata Abdullahi Adamu ya yi da gwamnoni su rika girmama magabatansu, kada su rainasu saboda mulki na hannunsu
  • Hakazalika ya yi kira ga tsaffin gwamnonin suyya don a zauna lafiyamulki a, wajibi ne suyi biyayya don a zauna lafiya

Abuja - Shugaba Uwar jam'iyyar All Progressives Congress APC, Senator Abdullahi Adamu ya tuhumi wasu tsaffin gwamnoni da gwamnoni masu ci da kokarin kawo baraka cikin jam'iyyar.

Adamu ya bayyana hakan ne a jawabin bude taron majalisar zartaswar jam'iyyar APC, NEC, dake gudana a Transcorp Hotel Abuja, rahoton Vanguard.

Abdullahi Adamu
Yanzu-yanzu: Tsaffin Gwamnoni da Gwamnoni masu ci ke raba kan 'ya'yan jam'iyya, Abdullahi Adamu Hoto; @BuhariSallau1
Asali: Twitter

Shugaba Muhammadu Buhari; mataimakinsa Yemi Osinbajo; Shugaban majalisar dattawa da na wakilai, Ahmad Lawan da Femi Gbajabiamila, duk suna hallare.

Kara karanta wannan

2023: Gaskiyar dalilin da ya hana Bola Tinubu halartan taron NEC na jam'iyyar APC

Adamu ya ce duk da cewa Gwamnoni ne jagororin jam'iyya a jihohinsu, ya kamata ru rika girmama tsaffin gwamnonin jihar.

Saboda a baya sune shugabanni kuma wajibi akwai mabiyansu da ba zasu so su ga an ci mutuncinsu ba.

Abinda ya hana Bola Tinubu halartan taron NEC na jam'iyyar APC, Rahman

Hadimin jagoran jam'iyyar APC na ƙasa, Bola Ahmad Tinubu, ta ɓangaren midiya, Tunde Rahman, ya bayyana dalilin rashin ganin ɗan takarar shugaban ƙasan a wurin taron majalisar ƙoli (NEC) na APC.

Hadimin Tinubun, ya kare uban gidansa ne a wata tattauna wa da wakilim jaridar Punch ranar Laraba.

Rahman ya ce kundin tsarin mulkin APC bai ba Bola Tinubu damar zuwa wurin taron ba kasancewar ba ya cikin majalisar NEC.

Ya ce:

Kara karanta wannan

Zulum ya yi rabon buhuhunan hatsi, kudi da atamfa ga mutum 100,000 a cikin garin Maiduguri da Jere

"Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ba mamba bane a majalisar NEC, shi ɗan majalisar mambobin APC ne. Mambobin NEC sun haɗa da shugaban ƙasa, mataimakinsa, shugaban majalisar dattawa."
"Sai kuma kakakin majalisar wakilai, shugabannin APC na jihohi da kuma mambobin kwamitin gudanarwa (NWC)."

Asali: Legit.ng

Online view pixel