2023: Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar APC ya kaɗu da jin kuɗin fam Miliyan N100m

2023: Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar APC ya kaɗu da jin kuɗin fam Miliyan N100m

  • Mai neman APC ta ba shi tikitin takarar shugaban ƙasa, Adamu Garba, ya kaɗu da jin kuɗin Fam ɗin takara Naira Miliyan N100m
  • Da yake martani kan kuɗin Fam, Matashin ɗan takarar ya nuna kaɗuwarsa da yawan su makudan kuɗin
  • A taron majalisar koli na jam'iyyar APC ta ƙasa, jam'iyya mai mulki ta yanke kudin Fam na kowace kujerar siyasa

Ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC, Adamu Garba, ya bayyana kaɗuwarsa ƙarara da jin tsabar kuɗin da jam'iyya ta sanya wa Fam ɗin sha'awar takara.

A yau Laraba yayin taron majalisar koli (NEC), jam'iyya mai mulkin ƙasar nan ta amince da sanya Naira Miliyan N100m a matsayin kudin Fam ɗin tsayawa takarar shugaban kasa.

Dan takara a APC, Adamu Garba.
2023: Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar APC ya kaɗu da jin kuɗin fam Miliyan N100m Hoto: @bbchausa
Asali: Twitter

Da yake tsokaci kan lamarin a shafinsa na dandalin sada zumunta Twitter, Garba, wanda ya nemi takara a 2019, ya rubuta cewa, "Miliyan N100m kuɗin Fam! Lallai."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Mataimakin Kwamishinan yan sanda ya yanke jiki ya mutu yana tsaka da aiki a Hedkwata

Matashin ɗan takaran wanda ke yawan amfani da dandalin sada zumuntan ya yi kira ga matasa su fito su yaƙi, "Jakunkunan kuɗi."

A cewarsa, "Ba zai yuwu a cigaba da siyan kujerun gwamnati a Najeriya ba, muna bukatar samun nagartattun shugabanni a 2023."

Martanin yan Najeriya

Sai dai wannan magana ta jawo hankulan yan Najeriya da dama, inda suka tofa albarkacin bakin su game da tsokacin matashin ɗan takaran.

@Irunnia_ ya rubuta cewa:

"Ko da ace ka sayar da manhajar Crew ɗinka, ba zaka iya haɗa kudin da suka zarce Miliyan biyu ba."

@I_amOD_SIT yace:

"Amma maganar gaskiya fa, ta ya wannan mutumin zai ayyana neman takara a jam'iyya amma bai san Farashin Fam ba? Hakan na nufin ba dagaske yake ba. Ina tantamar ya yi rijista da APC."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Tsohon na kusa da Buhari ya fice daga jam'iyyar APC, ya jero dalilai

@AfamDeluxo ya ce:

"Mafi sauki ka nemi mai kula da shafin Whatsapp, babu tsada."

@drpenking ya ce:

"Ina ga kaine kace manhajar Crowwe ba bu kamarta a faɗin Afirka, bai kamata miliyan N100m ta gagareka ba. Muje zuwa mu haɗu a bakin boda."

A wani labarin kuma Mataimakin Kwamishinan Yan Sanda Ya Yanke Jiki Ya Faɗi, Ya Mutu Yana Tsaka da Aiki a Ofis

Mataimakin kwamishinan yan sanda na jihar Bayelsa mai kula da sashin shugabanci ya rasu yana cikin aiki a Hedkwata.

Rahoto ya nuna cewa Mamacin ya yanke jiki ya faɗi a cikin Ofishinsa, aka yi kokarin kai shi Asibiti amma rai ya yi halinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262