Shugaban masu rinjaye a majalisar Bauchi ya karyata rade-radin barinsa APC zuwa PDP

Shugaban masu rinjaye a majalisar Bauchi ya karyata rade-radin barinsa APC zuwa PDP

  • Shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Bauchi, Tijjani Aliyu, yayi watsi da labaran cewa yana tuntuba domin barin APC zuwa PDP
  • Aliyu ya bayyana cewa shi dan jam’iyya ne na gaskiya don haka bashi da niyan bin kakakin majalisar jihar, Abubakar Suleiman zuwa jam’iyyar adawa
  • A makon jiya ne kakakin majalisar dokokin jihar ya sauya sheka daga APC zuwa PDP mai mulki a jihar

Bauchi - Akwai alamu masu karfi da ke nuna cewa wasu yan majalisar dokokin jihar Bauchi na iya bin sahun kakakin majalisar, Abubakar Suleiman zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) mai mulki a jihar, Nigerian Tribune ta rahoto.

A makon da ya gabata ne kakakin majalisar dokokin jihar ya sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) wacce ita ce mafi rinjaye a majalisar.

Kara karanta wannan

2023: APC ta rasa wani babban jigonta a jihar Oyo, ya sauya sheka zuwa PDP

Sai dai kuma, shugaban masu rinjaye a majalisar, Tijjani Mohammed Aliyu, ya nesanta kansa daga cikin wadanda ake rade-radin cewa za su bar APC.

Shugaban masu rinjaye a majalisar Bauchi ya karyata rade-radin barinsa APC zuwa PDP
Shugaban masu rinjaye a majalisar Bauchi ya karyata rade-radin barinsa APC zuwa PDP Hoto: Nigerian Tribune
Asali: UGC

Har ila yau ya kuma karyata batun cewa yana tuntube-tuntube a kan batun.

Da yake martani ga labaran jaridu da soshiyal midiya, Tijjani Aliyu wanda ke wakiltan mazabar Azare/Madangala a majalisar, ya bayyana cewa shi dan jam’iyya ne na gaskiya kuma bashi da niyan barin APC zuwa kowace jam’iyya, rahoton The Guardian.

A cewarsa:

“Ni dan jam’iyyar APC ne na gaskiya kuma bana tattaunawa da kowa. Mutanen da ke kusa dani sun sanni sarai. Ina watsi da wannan labarai na kafar watsa labarai saboda babu kamshin gaskiya a ciki.”

Kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi ya sauya sheka daga APC zuwa PDP

Kara karanta wannan

Abdulaziz Yari ya bayyana gaskiyar lamari game da batun sauya shekarsa daga APC zuwa PDP

A baya mun kawo cewa kakakin majalisar dokokin Bauchi, Rt. Hon. Abubakar Sulaiman, ya sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa Peoples Democratic (PDP) mai mulki a jihar, jaridar Punch ta rahoto.

Sulaiman ya lashe zabe a matsayin dan majalisa mai wakiltan mazabar Ningi a 2019 karkashin inuwar jam’iyyar APC.

Dan majalisar wanda ya kuma kasance shugaban kungiyar kakakin majalisun jiha ta Najeriya, ya sanar da batun sauya shekarsa a yayin shan ruwa na Ramadana wanda Gwamna Bala Mohammed ya shirya, wanda aka yi a gidan gwamnatin Bauchi a daren ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel