Dalilin da yasa 'yan APC ke kara yawan mabiya a Najeriya, inji ministan Buhari

Dalilin da yasa 'yan APC ke kara yawan mabiya a Najeriya, inji ministan Buhari

  • Jigo a jam'iyyar APC ya bayyana dalilin da yasa ake ganin jam'iyyar APC na kara habaka a kullum sabanin raguwa
  • Ya bayyana hakan ne yayin da yake karbar bakuncin wani jigo a jihar benue, wanda ya shigo jam'iyyar ta APC
  • Ya kuma bayyana cewa, ci gaban jam'iyyar APC na da nasaba ta kai tsaye da ci gaban da Buhari ya kawo

Jihar Benue - Ministan ayyuka na musamman da harkokin gwamnatoci, Sen. George Akume, ya ce mambobin jam’iyyar APC za su ci gaba da habaka saboda ci gaban da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu.

Akume ya bayyana haka ne a ranar Talata a garin Igbor da ke karamar hukumar Gwer a jihar Benue a lokacin da yake jawabi ga Amb. Yonov Agah, Darakta-Janar na Majalisar Tattaunawar Kasuwanci ta Najeriya da wasu mutane, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Tsohon na kusa da Buhari ya fice daga jam'iyyar APC, ya jero dalilai

Ministan Buhari, Geoge Akume ya yaba da aikin APC
Dalilin da yasa 'yan APC ke kara yawa a Najeriya, inji jigon APC Akume | Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Ministan ya ce Buhari ya taka rawar gani don haka ne ma mutanen da ba su da sha’awar siyasa ke fitowa a dandazonsu domin shiga jam’iyyar APC.

Ya ci gaba da cewa, jam’iyyar tana kuma karbar ‘yan wasu jam’iyyun siyasa da suke sauya sheka a kullum.

Ya kara da cewa:

“Za mu je garin Daudu da ke karamar hukumar Guma a Benue domin halartar bikin sauya sheka da zarar na kammala jawabina a nan.
"Muna danganta wannan gagarumin sauya sheka ga ci gaban da gwamnatin Buhari ta samu."

Ya zayyana wasu daga cikin ayyukan ci gaba na gwamnatin Buhari a Benue da suka hada da hanyar Makurdi-Abuja, hanyar Adoka-Naka-Makurdi, da kuma asibitin yara da haihuwa da ke Makurdi, da dai sauransu.

Ya kuma baiwa sabbin masu shigowa jam’iyyar tabbacin samun dama ba tare da la’akari da lokacin da suka zo jam’iyyar ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Jami'in tsaro daya ya mutu yayin da sojoji suka ragargaji 'yan bindiga a Neja

Ban shiga APC don tsayawa takara ba, Agah

A bangare guda, Agah, wanda tsohon Darakta ne na kungiyar kasuwanci ta duniya (WTO), ya ce bai shiga jam’iyyar domin neman wani mukami na siyasa ba, sai dai don hada karfi da karfe da Akume domin kwatowa, ‘yantar da jama’a da kuma ci gaban Benue.

Ya kuma bukaci jama’a da su zabi jam’iyyar APC a zabe mai zuwa na 2023, yana mai jaddada cewa jam’iyyar ce kadai za ta iya taimaka musu wajen cimma burinsu, kamar yadda Pulse ta tattaro.

Tun da farko, babban bako mai jawabi, Mista Mike Iordye, ya yi kira ga jama'a da su marawa jam’iyyar baya domin ci gaban al’umma baki daya.

Bidiyon yadda Ganduje ya kalli Wike ido cikin ido ya fada masa cewa ba zai kai labari ba a 2023

A wani labarin, Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya kalli takwaransa na jihar Ribas, Nyesom Wike a cikin ido sannan ya sanar masa da cewa ba zai yi nasara ba a kokarinsa na son gaje shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Yari da Marafa sun sauya sheka daga APC zuwa PDP

Ganduje ya yi sakin zancen ne a lokacin da Wike ya ziyarci jiharsa a yayin da yake ci gaba da tuntubar al’umman yankin arewacin Najeriya domin samun goyon bayansu.

Sai dai kuma cike da barkwanci, Gwamna Ganduje ya ce Wike na birge shi saboda kasancewarsa daga cikin mutane masu karfin gwiwa, wanda koda sun fadi a yau za su sake tashi domin sake gwada sa’arsu a gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel