Zaben 2023: Kwankwaso na shirin bayyana aniyarsa ta danewa kujerar Buhari

Zaben 2023: Kwankwaso na shirin bayyana aniyarsa ta danewa kujerar Buhari

  • A yau ne ake sa ran Kwankwaso zai bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa
  • Bayan dogon shawari, Kwankwaso ya ce alamu sun nuna akwai haske a wannan kuduri nasa na son gaje Buhari
  • A karshen makon da ya gabata ne ya ce zai sanar da 'yan Najeriya aniyarsa a hukumance domin neman goyon bayansu

Abuja - Bayan cece-kuce da shirye-shiryen siyasa, a yammacin yau (Talata) tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso zai bayyana sha'awar tsayawa takarar shugabancin kasa a jam'iyyar New Nigeria Peoples Party.

Jaridar Punch ta samu labari daga wani jigon jam’iyyar cewa jigon ‘yan siyasar daga yankin Arewa maso Yamma, mutumin Kano da sauran mabiyansa sun isa Abuja domin halartar taron.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi ya sauya sheka daga APC zuwa PDP

Aniyar Kwankwaso ta tsayawa takarar shugaban kasa a 2023
Zaben 2023: Kwankwaso na shirin bayyana aniyarsa ta danewa kujerar Buhari | Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

A cewar wani dan jam'iyyar:

"Mai martaba (Kwankwaso) yanzu ya kira ni, cewa zai bayyana aniyar takarar shugaban kasa a yau a Abuja."

An ruwaito cewa Kwankwaso, wanda kuma tsohon ministan tsaro ne, a watan Fabrairu ya sanar da kafa wata tafiyar siyasa mai suna National Movement (NM), domin sauya akalar yadda ake tafiyar da siyasa a Najeriya a zaben 2023.

Kamar makwanni biyu da suka gabata ne ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar PDP, inda ya bayyana dalilinsa da cewa, an mayar dashi saniyar ware da wasu dalilai da ba a rasa ba.

Sauran jiga-jigan tawagar NM sun hada da Sen. Suleiman Hunkuyi na jihar Kaduna; tsohon ministan matasa da raya wasanni, Solomon Dalung; Shahararren mai sukar gwamnati dan Arewa, Buba Galadima; da sauran fitattun 'yan Najeriya.

Kara karanta wannan

2023: Jigon APC Ya Faɗa Wa Ƴan Najeriya Irin Ƴan Siyasan Da Ya Kamata Su Ƙaurace Wa

A cewarsu, tawagar tasu za ta karbi mulki daga hannun jam’iyyar APC a zaben da za a gwabza a 2023.

Zan bayyana aniyar tsayawa takara a cikin makon nan, inji Kwankwaso

Jaridar Business day ta ruwaito cewa, Kwankwaso wanda ya zanta da manema labarai a karshen makon da ya gabata ya ce bayan kammala shawarwarin; zai sanar da ‘yan Najeriya kudirinsa na neman shugabancin kasar a hukumance.

A kalamansa:

“Ina ta neman shawarwarin abokai da ‘yan Najeriya masu ra'ayoyi daban-daban kuma sakamakon ya nuna akwai haske. Zan sanar da ‘yan Najeriya burina na siyasa a farkon mako mai zuwa."

To yau ne dai ake sa ran Kwankwason zai bayyana aniyar tasa kamar yadda ya shaidawa manema labarai.

Mai fada a ji ga Buhari: Ka san yadda zaka yi Jonathan ya gaje ka a zaben 2023

A wani labarin, Josiah Oyakonghan (da aka fi sani da Oyimi) ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya mikawa Goodluck Jonathan shugaban kasa a 2023 kasancewarsa dan yankin Kudu.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Jerin sunayen masu takarar shugaban kasa na APC da PDP

Oyimi dai shi ne tsohon jagoran rusasshiyar kungiyar Movement for the Emancipation of Niger Delta (MEND), kuma shugaban kungiyar Movement for the Actualization of the Dreams of Niger Deltans (MADND).

Jigon mai fada a ji ya yi wannan roko ne yayin ganawa da manema labarai, inda ya bayyana cewa, Goodluck Jonathan ne kawai ‘yan Najeriya za su iya amincewa ya warware musu dimbin matsalolin da ke damunsu, in ji rahoton Vanguard.

Asali: Legit.ng

Online view pixel