Da dumi-dumi: Kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi ya sauya sheka daga APC zuwa PDP

Da dumi-dumi: Kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi ya sauya sheka daga APC zuwa PDP

  • Kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi, Abubakar Sulaiman, ya fice daga jam'iyyar APC ya koma PDP
  • Suleiman wanda ya lashe zaben dan majalisa a karkashin APC a 2019 ya sanar da sauya shekar tasa a ranar Asabar a taron shan ruwa da gwamnan jihar ya shirya
  • Ya ce ya sauya sheka ne sakamakon irin shugabaci na Gwamna Mohammed da jajircewarsa wajen gyara jihar

Bauchi - Kakakin majalisar dokokin Bauchi, Rt. Hon. Abubakar Sulaiman, ya sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa Peoples Democratic (PDP) mai mulki a jihar, jaridar Punch ta rahoto.

Sulaiman ya lashe zabe a matsayin dan majalisa mai wakiltan mazabar Ningi a 2019 karkashin inuwar jam’iyyar APC.

Dan majalisar wanda ya kuma kasance shugaban kungiyar kakakin majalisun jiha ta Najeriya, ya sanar da batun sauya shekarsa a yayin shan ruwa na Ramadana wanda Gwamna Bala Mohammed ya shirya, wanda aka yi a gidan gwamnatin Bauchi a daren ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Tinubu ya tara duk shugabannnin Majalisan APC, sun yarda su mara masa baya a 2023

Da dumi-dumi: Kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi ya sauya sheka daga APC zuwa PDP
Da dumi-dumi: Kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi ya sauya sheka daga APC zuwa PDP Hoto: Auwal Garba
Asali: Facebook

Taron ya samu halartan manyan masu ruwa da tsaki na PDP daga kananan hukumomin Ningi, Toro, Warji da Dass na jihar.

A jawabin da ya yi wajen taron shan ruwa, an jiyo kakakin majalisar yana gabatar da shugaban jam’iyyar PDP a jihar, Hamsa Akuyam a matsayin “shugabar babbar jam’iyyarmu ta PDP.”

Suleiman ya ci gaba da cewa:

“Na san ana ta rade-radi, mutane na ta fadin cewa, na sauya sheka zuwa PDP, wasu sun ce karya ne bai sauya sheka ba.
“Amma a yau a wannan waje, ina mai farin cikin sanar da ku cewa yanzu ni dan PDP ne.”

Yana gama sanar da batun sauya shekarsa sai gaba daya taron ya kaure da murna.

A cewarsa, ya yanke shawarar komawa PDP ne a jihar sakamakon irin shugabaci na Gwamna Mohammed da jajircewarsa wajen gyara jihar.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Kakakin majalisar dokokin jihar Sokoto ya fita daga jam'iyyar APC, ya koma PDP

Ya kuma yabama gwamnan kan yadda yake tafiyar da alakar aiki da majalisar dokokin jihar duk da banbancin jam’iyya wanda hakan ke bashi damar aiwatar da manufofi da tsare-tsare don ci gaban jihar, Nigerian Tribune ta rahoto.

Gwamna Ganduje ya ba mukarrabansa daga nan zuwa gobe Litinin su ajiye mukamansu

A wani labari na daban, Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya umurci dukkanin wadanda ya baiwa mukaman siyasa da ke son yin takara a zaben 2023 da su ajiye aiki.

A cikin wata sanarwa daga babban sakataren labaransa, Abba Anwar, a ranar Lahadi, 17 ga watan Afrilu, Ganduje ya ce an baiwa masu mukaman tsakanin yanzu da Litinin, 18 ga watan Afrilu su yi murabus, Daily Nigerian ta rahoto.

Ya ce umurnin ya yi daidai da tanadin sashi 84(12) na sabuwar dokar zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel