Hotuna: Dan PDP Da Ya Sha Alwashin Sai Buhari Ya Yi Murabus Zai Yi Aski Ya Koma APC, An Masa Aski
- Wani dan jam'iyyar PDP mai suna Mustapha Zaki Yawuri da ya taba alkawarin ba zai aske gashin kansa ba sai Buhari ya yi murabus ya shiga jam'iyyar ta APC mai mulki a kasa
- Faruwar hakan yasa jam'ian jam'iyyar ta APC da suka tarbe shi suka yi masa aski domin masa maraba zuwa jam'iyyar duk da cewa Shugaba Buharin bai yi murabus
- Kamar yadda hotunan suka nuna, an ga mutumin zagaye da wasu maza a kalla takwas suna murmushi da raha da tafi yayin da daya cikinsu ke amfani da na'urar aski yana aske masa gashin kai
Wani dan babban jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, PDP, wanda ya yi alkawarin ba zai taba aske gashin kansa ba har sai Shugaba Buhari ya yi murabus ya koma All Progressives Congress, APC, kuma an masa aski.
Tsohon dan PDPn wanda aka bayyana sunansa a matsayin Mustapha Zaki Yawuri, ya koma APC ne a ranar Alhamis 28 ga watan Yuli, LindaIkeji ta rahoto.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Jami'an jam'iyyar APC da suka tarbe shi sun dage cewa sai ya aske gashin kansa tunda ya shigo jam'iyyar mai mulki a kasa.
Hakan yasa ya zauna aka kuma dakko na'urar aski wato 'kilipa' aka fara aske masa gashi yayin da mutanen da ke zagaye da shi ke murmushi da raha.
Ga dai hotunan a kasa:
Sanata Daga Arewa Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Baya Goyon Bayan Tsige Buhari
A wani rahoton, shugaban kwamitin labarai da wayar da kan kasa na majalisar dattawa, Danladi Sankara ya nesanta kansa daga shirin da ake yi na tsige Shugaba Muhammadu Buhari, rahoton Daily Trust.
Sanata Sankara, wanda ke wakiltar Jigawa North West a Majalisar ya kuma nesanta kansa daga shirin tsige shugaban majalisa, Ahmad Lawan.
Sanatocin jam'iyyun adawa, a ranar Laraba, bayan tattaunawa na away biyu sun bawa Buhari wa'adin wata shida ya magance matsalar tsaro ko kuma su tsige shi.
Asali: Legit.ng