Da dumi-dumi: Yari da Marafa sun sauya sheka daga APC zuwa PDP

Da dumi-dumi: Yari da Marafa sun sauya sheka daga APC zuwa PDP

  • Jam'iyyar APC ta rasa manyan jiga-jiganta biyu a jihar Zamfara, Abdulaziz Yari da Kabiru Marafa
  • Yan siyasar sun sauya sheka ne daga jam'iyyar mai mulki zuwa babbar jam'iyyar adamawa ta PDP
  • Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban PDP a Zamfara Kanal Bala Mande mai ritaya ya saki a ranar Lahadi, 17 ga watan Afrilu

Zamfara - Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Abdulaziz Yari da Sanata Kabiru Garba marafa sun sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Shugaban jam’iyyar adawa ta PDP a jihar, Ritaya kanal Bala Mande, ne ya sanar da hakan jim kadan bayan gama wani taron masu ruwa da tsaki a Gusau, babbar birnin jihar a ranar Lahadi, 17 ga watan Afrilu.

Da dumi-dumi: Yari da Marafa sun sauya sheka daga APC zuwa PDP
Da dumi-dumi: Yari da Marafa sun sauya sheka daga APC zuwa PDP Hoto: Daily Post
Asali: Twitter

Mande ya bayyana cewa sun zauna sannan sun yanke shawara kan batun sauya shekar Yari da Marafa sannan sun cimma yarjejeniyar aiki don ci gaban jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi ya sauya sheka daga APC zuwa PDP

Mande ya ce:

“Duk mun yarda za mu yi aiki don ci gaban jam’iyyar sannan PDP a jihar ta yi maraba da su a cikinta. Za mu tabbatar da gaskiya da adalci ga dukka mambobinmu har bayan mun lashe zabe a 2023.
“Za a sanar da ranar gagarumin bikin dawowarsu jam’iyyamu daga bisani amma za mu aiwatar da dukkan yarjejeniyar da muka cimma a yayin taron masu ruwa da tsaki.”

Sakataren labaran bangaren Yari na APC, Alhaji Ibrahim Muhammad Birnin Magaji, ya tabbatarwa Daily Trust da ci gaban amma bai yi karin bayani ba.

Magaji ya ce:

“Eh, da gaske ne za mu koma jam’iyyar adawa ta PDP, kuma iya abun da zan iya fadi kenan a yanzu.”

Kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi ya sauya sheka daga APC zuwa PDP

Kara karanta wannan

Da duminsa: Kakakin majalisar dokokin jihar Sokoto ya fita daga jam'iyyar APC, ya koma PDP

A wani labari makamancin wannan, munji cewa kakakin majalisar dokokin Bauchi, Rt. Hon. Abubakar Sulaiman, ya sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa Peoples Democratic (PDP) mai mulki a jihar, jaridar Punch ta rahoto.

Sulaiman ya lashe zabe a matsayin dan majalisa mai wakiltan mazabar Ningi a 2019 karkashin inuwar jam’iyyar APC.

Dan majalisar wanda ya kuma kasance shugaban kungiyar kakakin majalisun jiha ta Najeriya, ya sanar da batun sauya shekarsa a yayin shan ruwa na Ramadana wanda Gwamna Bala Mohammed ya shirya, wanda aka yi a gidan gwamnatin Bauchi a daren ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel