Da duminsa: Kakakin majalisar dokokin jihar Sokoto ya fita daga jam'iyyar APC, ya koma PDP

Da duminsa: Kakakin majalisar dokokin jihar Sokoto ya fita daga jam'iyyar APC, ya koma PDP

  • Jam'iyyar APC a jihar Sakkwato ta yi rashin manyan yan majalisar dokoki biyu a rana guda daya
  • Duk da cewa gwamnan jihar Sokoto PDP yake, Kakakin majalisar dokokin jihar da dimbin yan majalisar sun kasance a APC
  • Wannan ya biyo sauya shekan da wasu yan jam'iyyar APC ke yi zuwa PDP a jihar

Sokoto - Kakakin majalisar dokokin jihar Sakkwato, Aminu Muhammad Achida, ya sauya sheka daga jam'iyyar All Progressives Congress APC zuwa People’s Democratic Party PDP.

Hanarabul Achida ya gabatar da wasikar sauya shekarsa ne ranar Alhamis a zauren majalisa, rahoton Tvcnewsng.

Wani dan majalisa kuma mai wakiltar mazabar Wammako 2, Murtala Bello Maigona, shima ya bi sahun Kakakin, ya fita daga APC zuwa PDP.

Majalisar dokokin jihar Sokoto
Da duminsa: Kakakin majalisar dokokin jihar Sokoto ya fita daga jam'iyyar APC, ya koma PDP Hoto: Tvcnewsng
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Kotu ta bada umurnin garkame matasa biyu kan laifin 'ba haya' cikin Masallaci

Dubban 'yan APC da PDP a Katsina sun koma jam'iyyar su Kwankwaso NNPP

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa, sama da mambobin jam’iyyar APC da PDP 8,000 ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar NNPP a jihar Katsina.

Dubban mutanen, wadanda magoya bayan Hon Yazzi Muhammad ne da Hon Al-Amin Yahaya Sani, ‘yan takarar majalisar dokoki ta APC da PDP, sun gabatar da kansu ga shugabancin jam’iyyar NNPP a jihar baki daya.

A cewar Yazzi Muhammad sun yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar APC ne biyo bayan ganin sakamakon zaben kananan hukumomin da aka kammala wanda ya bayyana jam’iyyar APC a matsayin mara gaskiya da kishin ci gaban al’umma.

Al-Amin Yahaya ya ce ya koma jam’iyyar NNPP ne domin tabbatar da burinsa na wakiltar Katsina ta tsakiya a majalisar dokokin jihar, inda ya ce rashin gaskiya na PDP ya sa ya bar jam’iyyar zuwa NNPP.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel