Jerin kwamishanoni da hadiman Ganduje da sukayi murabus don takarar kujerar zabe

Jerin kwamishanoni da hadiman Ganduje da sukayi murabus don takarar kujerar zabe

A yau Lahadi, 17 ga watan Afrilu ne gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bukaci wadanda ya nada mukaman siyasa da ke da burin yin takara a babban zaben 2023 da su ajiye mukamansu.

Ganduje ya basu daga yanzu zuwa ranar Litinin, 18 ga watan Afrilu domin su gabatar masa takardun murabus din nasu.

Sai dai kuma, tun kafin wa’adin da ya diba masu ya cika, wasu daga cikin kwamishinoninsa sun yi murabus daga mukamansu.

Jerin kwamishanoni da hadiman Ganduje da sukayi murabus don takara kujerar zabe
Jerin kwamishanoni da hadiman Ganduje da sukayi murabus don takara kujerar zabe Hoto: Facebook/Abubakar Aminu Ibrahim/Labari24
Asali: UGC

A wannan rahoton, Legit Hausa ta zakulo maku jerin kwamishinoni da hadiman da suka ajiye aikinsu domin yin takarar kujerun daban-daban

1. Murtala Sule Garo – Kwamishinan karamar hukuma da harkokin sarauta zai yi takarar kujerar gwamnan jihar Kano karkashin jam’iyyar APC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Ganduje ya yi watsi da murabus din kwamishanoni 4, yace su koma bakin aiki, ga jerinsu

2. Musa Iliyasu Kwankwaso – Kwamishinan raya karkara zai yi tararar kujerar dan majalisar tarayya mai wakiltan mazabar Kura/Madobi/Garunmallam

3. Ibrahim Ahmad Karaye – Kwamishinan al’adu da yawon bude ido zai yi takarar kujerar dan majalisar tarayya mai wakiltan mazabar Karaye/Rogo

4. Nura Dankadai - Kwamishinan kasafin kudi zai yi takarar kujerar dan majalisar tarayya mai wakiltan mazabar Doguwa/Tudunwada

5. Sadiq Wali – Kwamishinan albarkatun ruwa zai yi takarar gwamna a karkashin jam’iyyar PDP

6. Dr. Aliyu Musa Aliyu Kibiya - Babban Darakta Hukumar Hisba ta Jihar Kano zai yi takarar kujerar Majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure

7. Hon. Sanusi Said Kiru - Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano zai yi takarar Majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Kiru da Bebeji a Jamiyyar APC

8. Dr. Mukhtar Ishaq Yakasai - Kwamishinan Ma'aikatar Ayyuka na Musamman na Jihar Kano zai yi takarar Majalisar Tarayya a Karamar hukumar Birni da Kewaye

Kara karanta wannan

Gwamna Ganduje ya amince da murabus din kwamishanoninsa 7, ga jerinsu

9. Hon. Mahmoud Muhammad Santsi - Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano zai yi takarar Majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Gabawa da Gezawa a Jamiyyar APC

10. Malam Ali Bullet - Mai Bawa Gwamna Shawara akan Harkokin Sufuri zai yi Takarar Majalisar Jiha mai wakiltar Karamar Hukumar Tudunwada a Jamiyyar APC

11. Hon. Abdullahi M Gwarzo Babangandu - MD Remasab zai yi Takarar Majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Gwarzo da Kabo a Jamiyyar APC

12. Dr. Nasiru Yusuf Gawuna - Mataimakin gwamnan jihar Kano ya yi murabus a matsayin kwamishinan noma

13. Farouq Sule Garo - Babban mai ba gwamna shawara kan kula da ayyuka zai yi takarar Majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Gwarzo da Kabo a Jamiyyar APC

14. Hon. Ado Tati Dala – Babban mai ba gwamna shawara kan harkokin dalibai zai yi takarar Kujerar Majalisar Jiha na Karamar hukumar Dala a Jamiyyar APC

Kara karanta wannan

Sunaye da jihohi: Kwamishinoni 53 sun yi murabus, ministocin Buhari masu takara sun yi mirsisi

15. Hon. Maifada Bello Kibiya – Mamba na din-din-din a hukumar fansho ta jihar Kano zai yi takarar Kujerar Majalisar Jiha na Karamar hukumar Kibiya a Jamiyyar APC

16. Dr. Aminu Ibrahim Tsnayawa - Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano zai yi takarar Kujerar Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Kunchi/ Tsanyawa a Jamiyyar APC

17. Dr. Ali Haruna Makoda - Shugaban Maaikatan Fadar Gwamnatin Jihar Kano zai yi takara a Jamiyyar APC

18. Hon. Kabiru Ado Lakwaya - Kwamishinan Matasa da wasanni na Jihar Kano zai yi takarar Kujerar Majalisar Tarayya na Karamar hukumar Gwarzo da Kabo a Jamiyyar APC

19. Hon. Lamin Sani - Mai Bawa Gwamna Shawara akan Harkokin Kananan Hukumomi da masarautu zai yi takarar Kujerar Majalisar Tarayya a Karamar Hukumar Nasarawa a Jamiyyar APC

20. Dr. Sabitu Y Shanono - Darakta Janar SACA zai yi Takarar Kujerar Majalisar Tarayya a Kananan Hukumomin Bagwai da Shanono a Jamiyyar APC

Kara karanta wannan

2023: A Manta Da Batun Zaɓe Bayan Saukan Buhari, a Kafa Gwamnatin Wucin Gadi Da Za Ta Saita Najeriya, Dattijon Ƙasa Ya Bada Shawara

21. Hon. Shuaibu Usman Anto - Mai Bawa Gwamna shawara akan Jam'iyyu zai yi Takarar Kujerar Majalisar Jiha a Karamar hukumar Dala a Jamiyyar APC

Gwamna Ganduje ya ba mukarrabansa daga nan zuwa gobe Litinin su ajiye mukamansu

Mun kawo a baya cewa Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya umurci dukkanin wadanda ya baiwa mukaman siyasa da ke son yin takara a zaben 2023 da su ajiye aiki.

A cikin wata sanarwa daga babban sakataren labaransa, Abba Anwar, a ranar Lahadi, 17 ga watan Afrilu, Ganduje ya ce an baiwa masu mukaman tsakanin yanzu da Litinin, 18 ga watan Afrilu su yi murabus, Daily Nigerian ta rahoto.

Ya ce umurnin ya yi daidai da tanadin sashi 84(12) na sabuwar dokar zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel