Gwamna Ganduje ya ba mukarrabansa daga nan zuwa gobe Litinin su ajiye mukamansu

Gwamna Ganduje ya ba mukarrabansa daga nan zuwa gobe Litinin su ajiye mukamansu

  • Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya bukaci duk wanda zai shiga takarar wata kujera a zaben 2023 da ya ajiye mukaminsa
  • Ganduje ya basu daga nan zuwa ranar Litinin, 18 ga watan Afrilu su ajiye masa mukaminsa kamar yadda sabuwar dokar zabe ta yi tanadi
  • Babban sakataren gwamnatin jihar ne ya fitar da sanarwar da yawun gwamnan a ranar Lahadi, 17 ga watan Afrilu

Kano - Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya umurci dukkanin wadanda ya baiwa mukaman siyasa da ke son yin takara a zaben 2023 da su ajiye aiki.

A cikin wata sanarwa daga babban sakataren labaransa, Abba Anwar, a ranar Lahadi, 17 ga watan Afrilu, Ganduje ya ce an baiwa masu mukaman tsakanin yanzu da Litinin, 18 ga watan Afrilu su yi murabus, Daily Nigerian ta rahoto.

Kara karanta wannan

Karfe 2 na dare, Zulum ya dira asibitin gwamnati na Monguno, zai kara 30% na albashi ga likitoci a LGs 7

Ya ce umurnin ya yi daidai da tanadin sashi 84(12) na sabuwar dokar zabe.

Gwamna Ganduje ya ba mukarrabansa daga nan zuwa gobe Litinin su ajiye mukamansu
Gwamna Ganduje ya ba mukarrabansa daga nan zuwa gobe Litinin su ajiye mukamansu Hoto: The Nation
Asali: UGC

Sanarwar ta ce:

“Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya umurci dukkanin masu rike da mukaman siyasa da ke son yin takarar kujeru a zaben 2023 mai zuwa da su yi murabus daga mukamansu.”

Daily Post ta rahoto cewa wasu kwamishinoni, hadimai da ma sakataren gwamnatin jihar na neman takarar mukamai daban-daban na gwamnati.

Tun farko dai kwamishinan Ganduje kan albarkatun ruwa, Sadiq Wali, ya yi murabus daga kujerarsa sannan ya yanki fom din takarar gwamna a karkashin jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, PDP.

Sai dai kuma, gwamnan ya ki yarda da murabus din Baffa Dan Agundi, shugaban hukumar KAROTA.

Sakataren Fadar Gwamnatin Jihar Ebonyi Ya Yi Murabus Daga Muƙaminsa, Ya Shiga Takara a 2023

Kara karanta wannan

Nayi matukar kaduwa bisa ambaliyar ruwan sama a kasar Afrika ta Kudu, Shugaba Buhari

A wani labari na daban, Sakataren gwamnatin jihar Ebonyi, Kenneth Ugbala, ya yi murabus daga kan kujerarsa domin maida hankali wajen cika burinsa na zama Sanata, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Mista Ugbala ya bayyana haka ga manema labarai bayan wani taron sirri da mambobin kwamitin gudanarwa na jam'iyyar APC reshen jihar Ebonyi a Sakatariyar jam'iyya dake Abakaliki.

Tsohon sakataren gwamnatin na hangen kujerar Sanata mai wakiltar mazaɓar Ebonyi ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya a zaɓen 2023 dake tafe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng