Ganduje ya yi watsi da murabus din kwamishanoni 4, yace su koma bakin aiki, ga jerinsu

Ganduje ya yi watsi da murabus din kwamishanoni 4, yace su koma bakin aiki, ga jerinsu

  • Akalla mutum 11 cikin kwamishanonin gwamnatin jihar Kano sun ajiye aikinsu makon da ya gabata
  • Gwamnan jihar ya amince da murabus din mutum bakwai cikinsu kuma yace sauran su koma bakin aikinsu
  • Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya umurci dukkanin wadanda ke da niyyar siyasa su ajiye mukaminsu bisa doka

Kano - Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya yi watsi da murabus din kwamishanoni shida cikin kwamishanoninsa da suka yi murabus don takarar kujerar siyasa a 2023.

Wannan ya bayyana a jawabin da sakataren yada labaran gwamnan, Abba Anwar, ya saki ranar Talata, 19 ga watan Afrilu, 2022.

A jawabin, gwamnan ya amince da na mutum bakwai cikin 11 da sukayi murabus, yace guda shida su koma bakin aiki.

Yace:

"An umurci shugaban ma'aikatan gidan gwamnati da duka sauran kwamishanonin su koma bakin aiki a ma'aikatunsu."

Kara karanta wannan

Gwamna Ganduje ya amince da murabus din kwamishanoninsa 7, ga jerinsu

Legit ta tattaro muku jerinsu:

1. Hon. Sanusi Said Kiru - Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

2. Nura Dankadai - Kwamishinan kasafin kudi

3. Dr. Aminu Ibrahim Tsnayawa - Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano zai yi takarar Kujerar Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Kunchi/ Tsanyawa a Jamiyyar APC

4. Dr. Ali Haruna Makoda - Shugaban Maaikatan Fadar Gwamnatin Jihar Kano zai yi takara a Jamiyyar APC

Gwamna Ganduje ya ba mukarrabansa daga nan zuwa gobe Litinin su ajiye mukamansu

Mun kawo a baya cewa Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya umurci dukkanin wadanda ya baiwa mukaman siyasa da ke son yin takara a zaben 2023 da su ajiye aiki.

A cikin wata sanarwa daga babban sakataren labaransa, Abba Anwar, a ranar Lahadi, 17 ga watan Afrilu, Ganduje ya ce an baiwa masu mukaman tsakanin yanzu da Litinin, 18 ga watan Afrilu su yi murabus, Daily Nigerian ta rahoto.

Ya ce umurnin ya yi daidai da tanadin sashi 84(12) na sabuwar dokar zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel