Gwamna Ganduje ya amince da murabus din kwamishanoninsa 7, ga jerinsu

Gwamna Ganduje ya amince da murabus din kwamishanoninsa 7, ga jerinsu

  • Gwamnatin jihar Kano ta bayyana jerin kwamishanonin jihar da aka amince su ajiye ayyukansu
  • Biyo bayan umurnin da gwamnan ya bada makon da ya gabata, akalla mutum 11 cikin kwamishanonin gwamnatin jihar ne suka ajiye aikinsu
  • Gwamnan jihar ya amince da murabus din mutum bakwai cikinsu kuma yace sauran su koma bakin aikinsu

Kano - Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya amince da murabus din kwamishanoni bakwai cikin kwamishanoninsa da suka yi murabus don takarar kujerar siyasa a 2023.

Wannan ya bayyana a jawabin da sakataren yada labaran gwamnan, Abba Anwar, ya saki ranar Talata, 19 ga watan Afrilu, 2022.

Gwamnan ya gode musu bisa gudunmuwar da suka baiwa jihar kuma yana musu fatan alheri.

Kara karanta wannan

Ganduje ya yi watsi da murabus din kwamishanoni 4, yace su koma bakin aiki, ga jerinsu

Yace:

"Mai girma gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, ya amince da murabus din wadannan kwamishanonin:

1. Dr. Nasiru Yusuf Gawuna - Mataimakin gwamnan jihar Kano ya yi murabus a matsayin kwamishinan noma

2. Murtala Sule Garo – Kwamishinan karamar hukuma da harkokin sarauta zai yi takarar kujerar gwamnan jihar Kano karkashin jam’iyyar APC

3. Ibrahim Ahmad Karaye – Kwamishinan al’adu da yawon bude ido zai yi takarar kujerar dan majalisar tarayya mai wakiltan mazabar Karaye/Rogo

4. Hon. Mahmoud Muhammad Santsi - Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano zai yi takarar Majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Gabawa da Gezawa a Jamiyyar APC

5. Dr. Mukhtar Ishaq Yakasai - Kwamishinan Ma'aikatar Ayyuka na Musamman na Jihar Kano zai yi takarar Majalisar Tarayya a Karamar hukumar Birni da Kewaye

Kara karanta wannan

Sunaye da jihohi: Kwamishinoni 53 sun yi murabus, ministocin Buhari masu takara sun yi mirsisi

6. Musa Iliyasu Kwankwaso – Kwamishinan raya karkara zai yi tararar kujerar dan majalisar tarayya mai wakiltan mazabar Kura/Madobi/Garunmallam

7. Hon. Kabiru Ado Lakwaya - Kwamishinan Matasa da wasanni na Jihar Kano zai yi takarar Kujerar Majalisar Tarayya na Karamar hukumar Gwarzo da Kabo a Jamiyyar APC

Gwamna Ganduje ya ba mukarrabansa daga nan zuwa gobe Litinin su ajiye mukamansu

Mun kawo a baya cewa Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya umurci dukkanin wadanda ya baiwa mukaman siyasa da ke son yin takara a zaben 2023 da su ajiye aiki.

A cikin wata sanarwa daga babban sakataren labaransa, Abba Anwar, a ranar Lahadi, 17 ga watan Afrilu, Ganduje ya ce an baiwa masu mukaman tsakanin yanzu da Litinin, 18 ga watan Afrilu su yi murabus, Daily Nigerian ta rahoto.

Ya ce umurnin ya yi daidai da tanadin sashi 84(12) na sabuwar dokar zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel