Da Dumi-Dumi: Awanni bayan Osinbajo ya ayyana shiga takara, Bola Tinubu ya sa Labule da gwamnonin APC

Da Dumi-Dumi: Awanni bayan Osinbajo ya ayyana shiga takara, Bola Tinubu ya sa Labule da gwamnonin APC

  • Jagoran jam'iyya mai mulki na ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya gana da gwamnonin cigaba na APC a birnin tarayya Abuja
  • Hakan na zuwa ne awanni kaɗan bayan mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ayyana tsayawa takara a 2023
  • Babu wani cikakken bayani kan abinda masu ruwa da tsakin APC suka tattauna amma ba zai zarce batun burin Tinubu ba

Abuja - Awanni kaɗan bayan mataimakin shugaban ƙasa ya bayyana sha'awar takarar shugaban ƙasa a 2023, Uban gidansa a siyasa, Bola Tinubu, ya sa labule da gwamnonin jam'iyyar APC.

Vanguard ta fahimci cewa taron wanda ba zai rasa nasaba da burin Tinubu na zama shugaban ƙasa na gaba ba, yana gudana ne a sirrance a gidan gwamnan Kebbi dake Asokoro, babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Kisan gilla: Wasu ‘yan bindiga sun kashe shugaban jam’iyyar APC a jihar Osun

Bola Tinubu tare da gwamnonin APC.
Da Dumi-Dumi: Awanni bayan Osinbajo ya ayyana shiga takara, Bola Tinubu ya sa Labule da gwamnonin APC Hoto: Jigawa State New Media Office/facebook
Asali: Facebook

Gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, shi ne shugaban kungiyar gwamnonin jam'iyyar All Progressive Congress wato APC.

A ranar Lahadi da daddare, mataimakin shugaban ƙasa, Osinbajo, ya gana da gwamnonin game da burinsa na neman takara a zaɓen 2023.

Shin duk gwanonin sun halarta?

A wata sanarwa da babban mai taimaka wa gwamnan Jigawa kan kafafen sada zumunta, Auwal D. Sankara, ya fitar ya ce jagoran APC na ƙasa ya gana da Muhammad Badaru na Jigawa da takwarorinsa.

Sauran gwamnonin da suka halarci taron sun haɗa da, Gwamna El-Rufai na jihar Kaduna, Simom Lalong na Filato, Abdullahi Ganduje na Kano da Atiku Bagudu na jihar Kebbi.

Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, gwamnan Imo, Hope Uzodinma, gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, gwamnan Osun, Gboyega Oyetola da gwamnan Ogun, Dabo Abiodun, duk sun halarci taron.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu, Amaechi da wasu jiga-jigan APC 4 da Osinbajo zai gwabza da su ya gaji Buhari

Taron Tinubu da gwamnoni.
Da Dumi-Dumi: Awanni bayan Osinbajo ya ayyana shiga takara, Bola Tinubu ya sa Labule da gwamnonin APC Hoto: Jigawa State New Media Office/facebook
Asali: Facebook

A wani labarin kuma Hotunan Katafariyar Gada Mai Hawa Uku da Ganduje Ke Ginawa a Kano, Babu Irinta a Faɗin Najeriya

Gwamnatin Kano na cigaba da aikin gada mai hawa uku a Shataletalen NNPC dake Anguwar Hotoro.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce suna sa ran kammala aikin zuwa watan Satumba, an raɗa wa Gadar 'Muhammadu Buhari Interchange.'

Asali: Legit.ng

Online view pixel