Da Dumi-Dumi: Ministan Sufuri, Amaechi, ya bayyana sha'awar gaje Buhari a 2023

Da Dumi-Dumi: Ministan Sufuri, Amaechi, ya bayyana sha'awar gaje Buhari a 2023

  • Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana aniyarsa ta gaje Buhari a zaɓen 2023 dake tafe karkashin APC
  • Tsohon gwamnan jihar Ribas ya ayyana kudirinsa a ranar Asabar a Filin wasa na Adokiye Amiesimaka Stadium dake jihar Ribas
  • Ministan ya kasance a gwamnati a muƙamai daban-daban tun bayan dawowar mulkin demokaraɗiyya a 1999

Rivers - Ministan sufuri na tarayyan Najeriya, Honorabul Rotimi Amaechi, ya ayyana shiga tseren takarar kujerar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.

Amaechi, wanda ya jima yana musanta raɗe-raɗin shiga takara, ya tabbatar da kudirinsa a hukumance ranar Asabar, 9 ga watan Afrilu, 2022.

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi.
Da Dumi-Dumi: Ministan Sufuri, Amaechi, ya bayyana sha'awar gaje Buhari a 2023 Hoto: Rt Hon Chibuike R Amaechi/facebook
Asali: Facebook

Ministan ya rubuta a shafinsa na dandalin sada zumunta Facebook cewa:

"Na tsaya a nan gaba gare ku ne domin na bayyana manufa ta kuma na sanar muku da bukata ta aiki a matsayin shugaban ku na gaba."

Tarihin siyasar Amaechi

Amaechi ya kasance a cikin gwamnati a muƙaman siyasa daban-daban tun bayan dawowar mulkin demokaraɗiyya a shekarar 1999.

Ya rike kujerar shugaban majalisar dokokin jihar Ribas na tsawon zango biyu daga 1999-2007, bayan haka ya kwashe shekara 8 a kan kujerar gwamnan Ribas daga 2007-2015.

Haka nan kuma Mista Amaechi na ɗaya daga cikin tsirarun ministocin da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya zarce da su bayan lashe zaɓe a karo na biyu a 2019.

Babu tantama yana ɗaya daga cikin Ministocin wannan gwamnatin da suka taɓuka abun a yaba, kuma shi ne jagoran yaƙin neman zaɓen Buhari a 2015 da 2019.

Tsohon gwamnan ya zama na farko daga cikin yan majalisar gwamnatin Buhari da ya shiga tseren, wasu na sha'awa amma har yanzun ba su ayyana aniyarsu ba.

A wani labarin kuma bayan Tambuwal, Bala Muhammed da Wike, wani gwamnan PDP ayyana aniyar shiga takarar shugaban ƙasa a 2023

Gwamnan Akwa Ibom, Udom Emmanuel, ya amsa kiran yan Najeriya na neman takarar shugaban ƙasa a 2023.

Gwamnan ya ce ya karbi Fam ɗin da wata kungiyar kare hakkin ɗan Adam ta siya masa na sha'awar takara a PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel