Da Dumi-Dumi: Na maida mutum 2,000 hamshaƙan Attajirai a Kogi, Yahaya Bello

Da Dumi-Dumi: Na maida mutum 2,000 hamshaƙan Attajirai a Kogi, Yahaya Bello

  • Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya ce idan APC ta amince masa zai dauki mace ta farko ta zama mataimakiyar shugaban ƙasa a 2023
  • Gwamna Bello ya ce gwamnatinsa ta canza rayuwar aƙalla mutum 2,000 zuwa hamshaƙan miliyoniya a Kogi
  • A ranar Asabar da ta gabata ya ayyana shiga tseren kujera lamba ɗaya karkashin inuwar jam'iyyar APC

Abuja - Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce gwamnatinsa ta maida aƙalla mutum 2,000 sun zama Miliyoniyoyi a jiharsa, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Ya yi wannan furucin ne a wurin taron ƙara wa juna sani game da manufofin GYB a siyasar Najeriya karo na biyu wanda ke gudana a Abuja.

Bello ya kuma bayyana shirinsa na zaɓar mace ta farko a matsayin mataimakiyar shugaban ƙasa idan APC ta lamunce masa ta bashi tutar takara a zaɓen 2023, kuma ta amince ya zaɓi wanda zasu tafi tare.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan ta’adda sun kai farmaki a jihar Neja, sun sace mutane da dama

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.
Da Dumi-Dumi: Na maida mutum 2,000 hamshaƙan Attajirai a Kogi, Yahaya Bello Hoto: Nigerian Air Force HQ/facebook
Asali: Facebook

Yayin da yake amsa tambaya kan tsarinsa game da tattalin arziƙin kasar nan, wanda ya haɗa da alƙawarin maida yan Najeriya miliyan N20m miliyoniyoyi zuwa 2030 idan ya gaji Buhari, gwamna Bello ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Mun maida mutane mafi ƙaranci mutum 2,000 sun zama Miliyoniyoyi a jihar Kogi."

Haka nan kuma game da wanda zai zaɓa su yi takara tare a matsayin mataimakin shugaban ƙasa, Bello ya ƙara da cewa:

"Idan aka bani damar na zaɓa da kaina, ba zan kauce wa tsagin jinsin mahaifiya ta ba. Zan so na tafi da mace ta farko a matsayin mataimakiyar shugaban ƙasa a 2023."

Yaushe gwamna Bello ya shiga takara a hukumance?

A ranar Asabar da ta gabata, gwamna Yahaya Bello, ya bayyana shiga tseren kujerar shugaban ƙasa a babban zaɓen 2023 dake tafe, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Kotu ta yi watsi da laifuka 8 cikin 15 da ake tuhumar Nnamdi Kanu da su

A wurin taron, Bello ya ɗauki alƙawarin ɗorawa daga ayyukan raya ƙasa da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya yi, da kuma aiwatar da tsarin Ibo na samar da Miliyoniyoyi tsakanin yan Najeriya.

A wani labarin kuma Mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, zai ayyana shiga takarar gaje Buhari a 2023

Wata majiya mai ƙarfi a fadar Aso Villa ta ce an kammala duk wasu shirye-shirye da ya kamata kan lamarin.

An jima ana yaɗa jita-jitar cewa Mataimakin shugaban zai nemi takarar kujera lamba ɗaya a Najeriya a babban zaɓen 2023 dake tafe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel