Mutane zasu fara cin ciyawa a Arewa saboda tsananin yunwa, Majalisar dinkin duniya

Mutane zasu fara cin ciyawa a Arewa saboda tsananin yunwa, Majalisar dinkin duniya

  • Majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa ana bukatar sama da naira bilyan 150 don ciyar da mutane a Arewa maso gabashin Najeriya
  • Jagoran UN dake Najeriya ya ce idan ba'a samu wannan kudi ba da yiwuwan su rika cin ciyawa
  • Ya ce sama da yan Najeriya milyan 8.4 ke bukata tallafi a Najeriya, kuma babu kudi

Abuja - Jagoran harkar tallafin majalisar dinkin duniya dake Najeriya, Matthias Schmale, ya bayyana cewa ana bukatar $351m don taimakawa al'ummar yankin Arewa maso gabas.

Matthias Schmale ya bayyana hakan ne ranar Juma'a a taron janyo hankali kan abinci da kiwon lafiya a birnin tarayya Abuja, rahoton TheCable.

Mutane zasu fara cin ciyawa a Arewa saboda tsananin yunwa, Majalisar dinkin duniya
Mutane zasu fara cin ciyawa a Arewa saboda tsananin yunwa, Majalisar dinkin duniya Hoto: @thecable
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Ba na shakkan Tinubu ko Osinbajo, duk zan kada su - Yahaya Bello

Ya ce sama da yan Najeriya milyan 8.4 ke bukata tallafi a Najeriya, kuma babu kudi.

A jawabinsa yace:

"A fadin Arewa maso gabashin Najeriya, mutum milyan 8.4 na bukatan tallafi. Abin takaici, rabin wannan mutane - 4.1m - zasu shiga halin bakin yunwa bana."
"Idan ba'ayi gaggawan samar da kudi ba, kimanin mutum milyan uku dake bukatan abinci na iya halaka."
"Rashin wannan taimako da bakin yunwa na iya jefa mutane karuwanci, amfani da kananan yara wajen ayyukan da sukafi karfinsu, da sayar da dukiyoyinsu."
"Na samu labarin cewa a bara, mutane a Arewa maso gabas na cin ciyawa don kada su muu. Ina tsoron hakan ya maimaita kansa idan bamu dau matakin gaggawa ba."

Ina muku maraba da watar Ramadana, ku baiwa talakawa abinci: Buhari ga Musulman Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari ya taya al'ummar Musulman Najeriya murnan ganin watar Ramadana bayan sanarwan Mai Alfarma Sarkin Musulmi.

Kara karanta wannan

Wutar lantarkin kasa ta sake lalacewa, Legas, Abuja Kaduna da wasu jihohi na cikin duhu

A sakon taya murnarsa, shugaba Buhari ya yi kira ga Musulmai su yi amfani da wannan dama wajen ciyar talakawa da marasa galihu.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki da yammacin Juma'a, 1 ga watan Afrilu, 2022.

Buhari yace lokacin azumi wani dama ne dake nunawa masu hannu da shuni irin yunwan da talaka ke fama da shi kulli yaumin.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel