Na amsa kiran yan Najeriya, Gwamnan Akwa Ibom ya shiga takarar shugaban ƙasa a 2023

Na amsa kiran yan Najeriya, Gwamnan Akwa Ibom ya shiga takarar shugaban ƙasa a 2023

  • Gwamnan Akwa Ibom, Udom Emmanuel, ya amsa kiran yan Najeriya na neman takarar shugaban ƙasa a 2023
  • Gwamnan ya ce ya karbi Fam ɗin da wata kungiyar kare hakkin ɗan Adam ta siya masa na sha'awar takara a PDP
  • Ya ce lokaci ya yi da kowane ɗan ƙasa zai ba da gudummuwa wajen gyara Najeriya a 2023

Akwa Ibom - Gwamna Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom, ya ce ya amsa kiran wasu yan Najeriya ta bakin kungiyar kare haƙƙin bil adama 'Brekete Family' na fitowa takarar shugaban ƙasa a 2023.

Emmanuel ya tabbatar da amincewa da kiran yan Najeriya ne a fadar gwamnati dake Uyo, ranar Alhamis da yamma, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Ya yi haka ne lokacin da kafar Talabijin da Radiyo Brekete Family Radio/TV ta miƙa masa Fam ɗin sha'awar takara na jam'iyyar PDP da ta siya masa kan Miliyan N40m.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta bayyana abinda zata yi don ceto Fasinjojin Jirgin ƙasan Abuja-Kaduna

Gwamnan Akwa Ibom, Udom Emmanuel.
Na amsa kiran yan Najeriya, Gwamnan Akwa Ibom ya shiga takarar shugaban ƙasa a 2023 Hoto: akstrending.com
Asali: UGC

Gwamnan ya miƙa godiya ga wanda ya kafa kafar labaran, Ahmed Isah, da sauran yan tawagarsa, waɗan da suka yi karo-karo suka siya masa Fam ɗin takarar kujera lamba ɗaya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Emmanuel ya nuna tsantsar farin cikinsa bisa yaƙini da kwarin guiwar da yan Najeriya suka nuna masa.

Premium Times ta rahoto a kalamansa ya ce:

"Na yaba da wannan karamci, ina mai tabbatar muku da cewa na amince da wannan Fam, na amince da Fam ɗin takarar shugaban ƙasa. Ba abin da yan Najeriya zasu haɗa kai su nema na yi watsi da shi."
"Gaskiya lokacin da na ji labarin kun fara shirin siya mun Fam, na tambayi kaina, ta ya zaku iya haɗa Miliyan N40m? Amma yau ga shi mafarkin ku ya zama gaskiya."
"Muna da mutane sama da miliyan 200m a Najeriya, amma kuka zaɓe ni don girmamawa, na ji ɗaɗi sosai, ina ƙara yaba wa wannan tawaga, sannan ina yaba wa yan Najeriya bisa kwarin guiwarsu a kaina."

Kara karanta wannan

2023: Ba zan janye ba, waya sani ko yan Najeriya ni suke mutuwar son na gaji Buhari, Ɗan takara a PDP

Zamu canza tsari a 2023

Gwamna Emanuel ya ɓata rai kan yanayin yadda sai mai ilimi me zurfi da kwarewa ke jagorantar wata kungiya, amma ace takardar Sakandire kaɗai ta isa ka shugabanci ƙasa mai mutum miliyan 200m.

Ya jaddada cewa irin waɗan nan dokokin dole a canza su a zaben 2023 domin samun nasarar matsar da Najeriya gaba.

Daga nan ya shawarci yan Najeriya su haɗa karfi da karfe wajen gayara Najeriya ta zama ƙasar da suke mafarki.

A wani labarin kuma Khadijat yar shekara 38 dake mafarkin gaje Buhari a 2023 ta shiga jam'iyya, ta faɗi wasu kalamai

Matashiya yar shekara 38, Khadijah Okunnu-Lamidi, ta tabbatar da shiga jam'iyyar SDP domin cika burinta.

Khadijat ta ayyana shiga tseren gaje kujerar shugaban ƙasa buhari a zaɓen 2023 amma ba ta shiga jam'iyya ba sai yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel