Ban sani ba ko za a yi zaben 2023 domin Allah bai sanar dani ba tukuna – Shahararren malamin addini

Ban sani ba ko za a yi zaben 2023 domin Allah bai sanar dani ba tukuna – Shahararren malamin addini

  • Shahararren faston Najeriya, Fasto Enoch Adeboye, ya ce har yanzu bai sani ba ko za a yi zabe a 2023
  • Malamin addinin ya ce Allah bai fada masa komai game da zaben na 2023 ba tukuna
  • Fasto Adeboye ya ce shi baya goyon bayan kowani dan takarar shugaban kasa a babban zaben kasar mai zuwa

Punch ta rahoto cewa Shugaban cocin Redeemed Christian Church of God, Fasto Enoch Adeboye, ya ce har yanzu bai sani ba tukuna ko za a yi babban zaben 2023.

Malamin addinin mai shekaru 80 a duniya ya ce Allah bai fada masa ko za a yi wani zabe ba a shekara mai zuwa.

Ya ce Allah ya yi masa magana game da zaben 2019 fiye da shekara guda kafin zaben amma a wannan karon bai aikata hakan ba a kan zaben 2023.

Kara karanta wannan

Dalilan Osinbajo na kin yarda Amaechi ya kashe N3.7b wajen tsare hanyar jirgin kasa

Ban sani ba ko za a yi zaben 2023 domin Allah bai sanar dani ba tukuna – Shahararren malamin addini
Fasto Adeboye ya ce bai sani ba ko za a yi zaben 2023 domin Allah bai sanar da shi ba tukuna Hoto: Pulse Nigeria

Sai ya gaggauta kara cewa Allah na iya yi masa magana game da zaben 2023 amma dai bai yi masa maganar ba tukuna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Malamin ya ce ya fi damuwa da kashe-kashen Kaduna, satar mai, tarin bashin da ke kan Najeriya da sauran matsalolin da suka yiwa kasar katutu a yanzu.

Adeboye ya kuma bayyana cewa siyasa ba tsarinsa bane kuma ba zai taba zama dan siyasa ba.

Ya kara da cewa shi baya goyon bayan kowani dan takarar shugaban kasa gabannin babban zaben 2023.

Babban faston ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 3 ga watan Afrilu a wajen taron yabon cocinsa na wata-wata.

Adeboye ya ce wannan bayanin yana da mahimmanci a yayin da ake tsaka da sukar cocin kan samar da Darakta na Siyasa da kuma umurtan mambobinsu da su shiga siyasa a 2023.

Kara karanta wannan

Amaechi: Dama na yi hasashen za a kawo hari a jirgi, na nemi kayan tsaro amma aka hana

Najeriya bata taba samun shugaban kasa irin Buhari ba tun daga 1914, in ji wani gwamnan arewa

A wani labarin, gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin shugaba mafi nagarta da Najeriya ta taba samu.

Masari ya bayyana cewa tun bayan hade Najeriya a 1914, kasar bata taba samun gwamnati mai inganci da shugaban kasa kamar Buhari ba, Premium Times ta rahoto.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 2 ga watan Afrilu, a Katsina yayin wani gangami da wadanda suka amfana da shirin tallafi na gwamnatin tarayya wato NSIP a jihar suka shirya, rahoton PM News.

Asali: Legit.ng

Online view pixel