Tsohon ɗan takarar gwamnan Kano, Abba Gida-Gida ya fice daga jam'iyyar PDP

Tsohon ɗan takarar gwamnan Kano, Abba Gida-Gida ya fice daga jam'iyyar PDP

  • Tsohon ɗan takarar gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya tabbatar da ficewa daga babbar jam'iyyar hamayya PDP a hukumance
  • Fitaccen ɗan siyasan wanda ya fi shahara da Abba Gida-Gida ya koma NNPP mai kayan marnari, yace PDP da APC duk kanwar ja ce
  • A cewarsa ya ɗauki matakin ne domin mutane suna ta habo-habon su koma domin NNPP ce zata iya ceto Najeriya

Kano - Ɗan takarar da jam'iyyar PDP ta tsayar a zaɓen gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda ya fi shahara da Abba Gida-Gida, ya koma jam'iyyar NNPP a hukumance, kamar yadda Daily Nigerian ta rahoto.

Mista Yusuf, wanda ya samu goyon bayan tsohon gwamna, Rabiu Musa Kwankwaso, ya sha kaye ne a hannun gwamna mai ci, Dakta Abdullahi Umar Ganduje a zaɓen 2019.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Abba Gida-Gida ya sauya sheka daga PDP zuwa NNPP

Abba Gida Gida.
Tsohon ɗan takarar gwamnan Kano, Abba Gida-Gida ya fice daga jam'iyyar PDP Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Mutane na ganin zaɓen cike yake da tashin tashina da kuma zargin maguɗi, wanda har sai da ta kai aka yi zagaye na biyu bayan INEC ta bayyana shi da wanda bai Kammalu ba.

Ana zaton Tsohon gwamnan Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Kwankwaso zai koma NNPP a hukumance ranar 30 ga watan Maris, 2022.

PDP ba ta da maraba da APC - Abba Gida-Gida

A jawabinsa a wurin sauya sheka zuwa NNPP a gundumarsa Diso ƙaramar hukumar Gwale, Abba Gida-Gida ya ce jam'iyyar PDP ba ta da maraba da APC mai mulki, duk kanwar ja ce.

Ya bayyana cewa PDP ta yaudari mutanenta da kuma jagora a Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso, duk da ruwan kuri'un da suka yi wa jam'iyyar a zaɓen 2019.

Kara karanta wannan

Yanzu adadin mambobin jam'iyyar APC milyan 41 a Najeriya, Mai Mala Buni

A cewarsa, wannan matakin da ya ɗauka ya zama wajibi a kansa duba da yadda mutane ke Alla-Allah, suna kira a koma jam'iyyar NNPP.

Abba Gida-Gida ya ce jam'iyyar NNPP na da ƙudiri da manufa masu kyawu da zasu iya ceto Najeriya daga wannan halin, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

A wani labarin na daban kuma Dubun wani ƙasurgumin shugaban yan bindiga da ya addabi hanyar Kaduna-Abuja ya cika

Hukumar yan sandan ƙasar nan, ranar Alhamis, ta sanar da kame wani gawurtaccen ɗan bindiga da wasu mutum 26.

A cewar yan sandan, mutumin mai suna Yellow Ashana, ya amsa cewa su ke addabar matafiya a hanyar Kaduna-Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel