Da dumi-dumi: Abba Gida-Gida ya sauya sheka daga PDP zuwa NNPP

Da dumi-dumi: Abba Gida-Gida ya sauya sheka daga PDP zuwa NNPP

  • Abba Gida-Gida ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa NNPP gabannin babban zaben 2023
  • Tsohon dan takarar kujerar gwamnan na jihar Kano a zaben 2019 ya sauya shekar ne gabannin Ubangidansa, Rabiu Kwankwaso
  • Ya ce ya sauya shekar ne saboda kiraye-kirayen da miliyoyin al'umma su ke yi na ya koma NNPP, wacce ta ke da manufofi ceto yan kasa da ga mawuyacin halin da suke ciki

Dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben gwamnan jihar Kano na 2019, Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida ya koma jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Daily Nigerian ta rahoto.

Abba Gida-Gida, wanda ya samu goyon bayan tsohon gwamnan jihar, Rabiu Kwankwaso, ya sha kaye a zaben na 2019, bayan gwamna Abdullahi Ganduje ya koma kan kujerarsa.

Kara karanta wannan

Tsohon ɗan takarar gwamnan Kano, Abba Gida-Gida ya fice daga jam'iyyar APC

Da dumi-dumi: Abba Gida-Gida ya sauya sheka daga PDP zuwa NNPP
Abba Gida-Gida ya sauya sheka daga PDP zuwa NNPP Hoto: Labarai24
Asali: UGC

Ana sanya ran Kwankwaso ma zai koma jam’iyyar a ranar 30 ga watan Maris, sannan daga bisani sai ayyana aniyar takarar kujerarshugaban kasa a karkashin jam’iyyar.

A jawabinsa a wajen ayyana sauya shekarsa a unguwar Diso da ke karamar hukumaer Gwale na jihar Kano, Yusuf ya ce PDP bata da banbancin da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce jam'iyar ta ci amanar al'ummar Kano da jagoranta, Rabi'u Musa Kwankwaso duk da irin tarin kuri'u da su ka kada mata a zaben 2019.

A cewarsa, matakin sauya shekar ya zama dole duba da irin kiraye-kirayen da miliyoyin al'umma su ke yi na ya sauya jam'iyyar NNPP, wacce ta ke da manufofi na gaskiya na tserar da yan kasa da ga mawuyacin halin da su ke ciki.

Sabon Ƙalubale Na Jiran Kwankwaso Idan Ya Bar PDP Zuwa NNPP, Zai Ci Karo Da Abokan Takara 15

Kara karanta wannan

Yanzu adadin mambobin jam'iyyar APC milyan 41 a Najeriya, Mai Mala Buni

A wani labari, sakataren watsa labaran jam’iyyar New Nigerian People’s Party (NNPP), Ambasada Agbo Major ya ce akwai ‘yan takarar shugaban kasa 15 da ke son tsayawa karkashin jam’iyyar.

Ya kara da bayyana cewa akwai ‘yan takarar gwamna, sanata, ‘yan majalisar tarayya da ‘yan majalisar jiha da yawa da suke da burin tsayawa karkashin inuwar jam’iyyar.

Ambasada Agbo ya ce za su shirya gangamin jam’iyyar a ranar 30 ga watan Maris kuma za a yi gangamin ne a Abuja kamar yadda ya sanar da manema labarai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel