Yanzu-Yanzu: Wani Magoyin Bayan APC Ya Mutu Yayin Babban Taron Jam'iyyar a Abuja

Yanzu-Yanzu: Wani Magoyin Bayan APC Ya Mutu Yayin Babban Taron Jam'iyyar a Abuja

  • Wani bawan Allah cikin magoya bayan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya yanke jiki ya fadi a yayin babban taron a Abuja
  • Wasu mutane da ke kusa da shi sun bayyana cewa ya koka yana ganin jiri sannan daga bisani kawai sai aka ga ya yanke jiki ya fadi
  • Mutane sun garzaya sun kai masa dauki amma hakan bai yi nasara ba inda ya ce ga garinku, jami'an tsaro da wasu suka fita da gawarsa

FCT, Abuja - Wani mai goyon bayan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya yanke jiki ya fadi a yayin taron gangamin jam'iyyar da aka yi ranar Asabar.

Magoyin bayan jam'iyyar yana hanyar zuwa Eagle Square ne, wurin da ake taron, a lokacin da ya yanke jiki ya fadi ya kuma mutu, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Azumin Ramadan: Sarkin Musulmi ya yi gargadi kan kara farashin kayan masarufi

Yanzu-Yanzu: Wani Mai Goyon Bayan APC Ya Mutu Yayin Babban Taron Jam'iyyar a Abuja
Wani Mai Goyon Bayan APC Ya Mutu Yayin Babban Taron Jam'iyyar a Abuja.
Asali: Original

Ya koka cewa yan jin jiri

Daya daga cikin wadanda suke kusa da mammacin sun ce ya koka da cewa yana ganin jiri sannan daga bisani ya yanke jiki ya fadi.

Wakilin Daily Trust da ke wurin ya ga yadda magoya bayan jam'iyyar da dama suka garzaya inda ya ke don kai masa dauki amma ba su yi nasara ba.

Daga bisani an rufe mammacin sannan wasu mutane tare da jami'an tsaro suka fice da gawarsa.

Hadimin El-Rufai Ya Koma Jam'iyyar PDP, Zai Yi Takarar Gwamna a 2023

A wani labarin, Jimi Lawal, Mashawarci na muamman ga gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, kan habbaka saka hannun jari, ya shiga jam'iyyar PDP a Jihar Ogun, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Taron gangamin APC: N300 ake siyar da ruwan goran N100 a wajen taron

Lawal, wanda ya ziyarci sakatariyar PDP a Abeokuta, ranar Asabar, ya kuma ayyana niyarsa na yin takarar gwamna a zabe da ke tafe.

Ma'aikacin bankin da ya samu horaswa a Landan ya nemi kujerar gwamna a karkashin APC a zaben 2019, amma ya sha kaye hannun Gwamna Dapo Abiodun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164