2023: Jam’iyyun siyasa 5 sun shirya mikawa Tinubu tikitin takarar shugaban kasa – Kungiyoyin arewa
- Kungiyoyin arewa ta tsakiya 200 sun nuna goyon bayansu ga takarar shugabancin Bola Tinubu
- Kungiyar NCAT ta ce jam'iyyun siyasa sun shirya tsaf domin ba jagoran na APC tikitin takarar shugaban kasa idan jam'iyyarsa ta hana shi
- Shugaban kungiyar, John Ali Oriri, ya bayyana a wajen taron cewa mahalarta taron sun yi nazari sosai kan takarar Tinubu
Abuja - Kimanin kungiyoyi 200 daga arewa ta tsakiya ne suka nuna goyon bayan takarar jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, domin zama shugaban kasa a 2023.
Kungiyar karkashin inuwar ‘North Central Agenda for Tinubu’ ta ce jam'iyyun siyasa sun shirya ba tsohon gwamnan na jihar Lagas tikitin takara kai tsaye idan APC ta ki tsayar da shi a matsayin dan takararta a 2023, jaridar Punch ta rahoto.
Kungiyar NCAT ta bayyana hakan ne a cikin wata takarda da ta saki a Abuja bayan taronta wanda ya samu halartan wakilai da shugabannin kungiyoyi 200 daga arewa ta tsakiya a ranar Talata.
Ta ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Kungiyoyin sun gano tare da shirya wasu jam’iyyun siyasa biyar da za su baiwa Tinubu tikiti kai tsaye a matsayin dan takararsu na shugaban kasa idan APC ta ki yin abun da ya kamata.”
Shugaban NCAT, John Ali Oriri, ya bayyana a wajen taron cewa mahalarta taron sun yi nazari sosai kan takarar Tinubu da kuma tasirin nasarar da zai samu a takarar shugaban kasa.
Vanguard ta nakalto kungiyar na cewa:
“Tinubu ne zabinmu daga jerin ’yan takarar da suka nuna sha’awar shugabancin Najeriya.
“Asiwaju Ahmed Bola Tinubu ya ayyana aniyarsa ta yin takarar shugaban kasa a 2023 a karkashin inuwar APC, Sauran yan takara a APC da sauran jam’iyyun siyasa suma sun nuna ra’ayinsu kan wannan kujera.
“Asiwaju Tinubu ya fara tuntubar masu ruwa da tsaki daban-daban da kungiyoyi a fadin kasar, inda a nan yake ci gaba da bayyana manufarsa na son daura Najeriya kan turbar daurewar tattalin arziki da kuma tabbatar da matsayin kasar nan a harkokin duniya.
"Tsohon gwamnan na jihar Lagas ya tabbatar da cewar shi babban manaja ne mai kula da albarkatun kasa, musamman ma’aikata, domin ya horar da shugabannin siyasa da suka kawo sauyi nagari a Najeriya ta hanyar mukaman da suka rike ko kuma wanda suke rike da su har yanzu.
“Tinubu na da tarin kwarewa da kasar ke bukata a shugabanta na gaba. Bai kamata a wofantar da wadannan manyan siffofi ba don mutanen da kawai suke son cimma ajandar karan kansu don lalata kasar gabaki daya.”
Oriri ya ce akwai muhawara da ke gudana game da shiyya-shiyya, inda aka karkata akalar ra'ayi na ganin yankin Kudancin kasar ya samar da shugaban kasa na gaba.
Zaben 2023: 'Yan Najeriya ke son na tsaya takara, ba wai son raina bane, inji Atiku
A wabi labarin, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abukabar ya bayyana cewa yan Najeriya ne suka nemi ya tsaya takarar shugaban kasa a babban zaben 2023.
Atiku ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Talata, 22 ga watan Maris, kwana guda kafin ya ayyana takararsa a hukumance.
Atiku ya kuma ce zai yi takara ne saboda kawo wa alumman kasar sauki kan matsalolin da suke fuskanta.
Asali: Legit.ng