Da Dumi-Dumi: Sanata Uba Sani ya bayyana shirinsa na takarar gwamnan Kaduna a 2023

Da Dumi-Dumi: Sanata Uba Sani ya bayyana shirinsa na takarar gwamnan Kaduna a 2023

  • Sanata Uba Sani mai wakiltar Kaduna ta tsakiya ya shiga tseren takarar gwamnan Kaduna a 2023 dake tafe
  • Sanatan ya faɗi haka ne yayin da yakai ziyara Sakatariyar APC ta jiha, a cewarsa ya je ne domin neman goyon bayan shugabanni
  • Gwamna El-Rufa'i na Kaduna ya ce wanda zai gaji kujerarsa na cikin tawagarsa 11 na farko da suka yi aiki tare tun 2014

Kaduna - Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya majalisar dattawan Najeriya, Sanata Uba Sani, ya bayyana sha'awar neman takarar gwamnan Kaduna a 2023.

Sanatan ya bayyana haka ne a Sakatariyar jam'iyyar APC ta jihar Kaduna ranar Talata, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.

Sanata Uba Sani na jihar Kaduna
Da Dumi-Dumi: Sanata Uba Sani ya bayyana shirinsa na takarar gwamnan Kaduna a 2023 Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A bayaninsa, Sanata ya ce ya ziyarci Sakatariyar jam'iyya ne domin neman goyon bayansu da kuma haɗin kai wajen cimma kudirinsa na ɗarewa kujerar gwamna.

Kara karanta wannan

Takara a 2023: Ɗiyar Bola Tinubu ta yi tsokaci kan shirin mahaifinta na gaje kujerar Buhari

A kalamansa, Sanata Sani ya ce:

"Na zo nan ne na sanar da ku manufata na neman takarar kujerar gwamnan Kaduna ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC. Ina bukatar goyon bayan ku har mafarkina ya zama gaskiya."

Sanatan ya kuma yaba wa gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i, bisa jan ragamar Kaduna zuwa mataki na gaba.

Ko Malam Nasiru na da wanda yake so ya gaje shi?

Da aka tambaye shi ko yana da wanda zai tsayar ya gaji kujerar gwamna a 2023, lokacin da ya zanta da Channels tv a shirin 'Siyasa a Yau' El-Rufa'i ya ce zaɓinsa na cikin tawagar makusantansa.

Ya ce:

"Zaɓi na ga yan Kaduna na cikin tawagar makusanta na, ina nufin 11 na farko, na kira su tawagata ne saboda akwai waɗan da muka yi faɗi tashi tare tun 2014, muka haɗa jam'iyya, muka nemi zabe, kuma aka zaɓe mu."

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Matar Abba Kyari ta yanke jiki ta fadi a cikin kotu

Sanata Sani na ɗaya daga cikin tawagar mutum 11 na farko, kasancewar ya yi aiki a matsayin mai ba da shawara kan harkonin siyasa ga Malam El-Rufa'i daga 2015-2019.

Sai dai bayan haka ya yi murbus kuma ya nemi takarar Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya har ya samu nasara bisa goyon bayan Malam El-Rufa'i.

A wani labarin kuma Gwamna ya sallami baki ɗaya kwamishinoni da hadiman gwamnatinsa daga bakin aiki

Gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, ya sanar da rushe baki ɗaya mambobin kwamitin zartarwa na gwamnatinsa.

Gwamnan ya ɗauki matakin ne yayin da yake shirin miƙa nulki ga sabuwar gwamnati karkashin zababben gwamna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel