Sanatoci ga INEC: Ya kamata fursunoni a Najeriya su kada kuri'a a zaben 2023
- Majalisar dattawan Najeriya ta caccaka tsinke kan yiwuwar ba fursunoni damar kada kuri'a a zabukan kasar nan
- Majalisar ta bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC da ta duba kundin tsarin mulki wajen tabbatar da zaben fursunoni
- Hakazalika, majalisar ta ce ya kamata a duba yiwuwar kai rumfunan zabe zuwa ga gidajen yari a kasar nan
FCT, Abuja - Majalisar Dattawa ta bukaci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta bai wa fursunonin da suka cancanta damar kada kuri’a a duk zabukan kasar nan, rahoton Channels Tv.
Majalisar ta tattauna hakan ne a zamanta na ranar Talata a lokacin da ta yi nazari kan kudirin ba da dama ga fursunoni don kada kuri’a a babban zabe a Najeriya wanda Sanata Abba Moro ya dauki nauyi.
Sun yi kira ga INEC da ta tantance matsayin fursunonin da kundin tsarin mulki ya amince da rajistarsu a matsayin wadanda suka cancanci kada kuri’a kuma su kada kuri’a a lokacin zabe.
Sun bukaci INEC da duk hukumomin da abin ya shafa da su wayar da kan masu kada kuri’a a gidajen yari a Najeriya, domin wayar da kansu kan sanin ‘yancinsu da kuma wajibcin yin amfani da ikonsu a lokacin zabe.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Majalisar ta ce ya kamata INEC tare da hadin gwiwar hukumar gyaran hali ta Najeriya su samar da wuraren kada kuri’a a cibiyoyin da ake tsare da fursunoni a fadin kasar domin saukakawa fursunoni kada kuri'a, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Majalisar dattawan ta kuma bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ta bai wa wadanda suka cancanta a gidan yari damar yin rajistar kada kuri'a a duk fadin Najeriya.
Balle gidan yari: Jami'an tsaro sun sheke fursunoni 4, jami'i 1 ya jigata a kurkukun Osun
A wani labarin, 'yan gidan fursuna hudu sun sheka lahira a gidan gyaran hali na Najeriya da ke yankin Kosere da ke Ile-Ife a wani yunkurin balle gidan da suka yi.
Wani babban jami'in tsaro, wanda ya bukaci a boye sunansa, ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Ile-Ife a ranar Talata, Premium Times ta ruwaito.
Jami'in ya ce wasu mazauna gidan fursunan sun yi yunkurin tserewa a yayin da suke aikin tsaftace gidan da safe, a hakan ne suka raunata wani jami'i.
Asali: Legit.ng