2023: Magoya Bayan Yahaya Bello Sun Yi Wa Ganduje Zazzafan Martani Kan Cewa Arewa Na Goyon Bayan Tinubu

2023: Magoya Bayan Yahaya Bello Sun Yi Wa Ganduje Zazzafan Martani Kan Cewa Arewa Na Goyon Bayan Tinubu

  • Wata kungiyar matasa magoya bayan takarar shugabancin kasar Gwamnan Kogi Yahaya Bello a 2023 ta yi wa Ganduje zazzafan martani
  • Kungiyar ta bayyana cewa kalaman da aka danganta da gwamnan na Kano ba gaskiya bane na cewa arewa tana goyon bayan takarar shugabancin kasa na Bola Tinubu
  • Kungiyar ta ce zancen shaci fadi ne kawai domin kididigarsu ta nuna mafi yawancin masu zabe na gaskiya suna goyon bayan Yahaya Bello ya zama shugaban kasa a 2023

Kungiyar matasa masu goyon bayan takarar shugabancin kasa na Yahaya Bello a 2023, ta yi watsi da ikirarin da Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya yi na cewa Arewa tana goyon bayan takarar shugabancin jagoran APC, Ahmed Bola Tinubu don zama shugaban kasa.

Salihu Magaji, shugaban kungiyar na kasa ne ya yi watsi da ikirari na Ganduje cikin wata sanarwa da ya fitar kamar yadda The Sun ta rahoto.

Kara karanta wannan

Shin za ka tsaya takara a 2023: Jonathan ya ba da amsar da ba a yi tsammani ba

2023: Arewa ba ta goyon bayan Tinubu, Magoya bayan Yahaya Bello sun yi wa Ganduje martani
2023: Arewa ba ta tare da Tinubu, Magoya bayan Yahaya Bello sun yi wa Ganduje martani. Hoto: The Nation
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Magaji ya ce zancen na Ganduje 'shaci fadi ne kawai' kuma ba gaskiya bane sannan ba matsayin arewa ba kenan.

Ya yi mamaki yana mai cewa bai san ko jihohin arewa guda nawa Ganduje ya ziyarta ba kafin ya cimma wannan matsayar.

Wani sashi na jawabinsa:

"Bai tafi ko ina ba. Kungiyoyi siyasa na ainihi masu kima da ke hulda da talakawa a arewa suna da kididiga da ke nuna cewa arewa na tare da Yahaya Bello a burinsa na takarar shugaban kasa. Muna tuntubar mafi yawancin masu zabe da ke da katin PVC kuma sun shirya zaben Yahaya Bello a matsayin shugaban kasar Najeriya a 2023.
"Muna tsammanin Tinubu a matsayinsa na jagoran APC ya hada kan jam'iyya ya bari demokradiyya ta yi halinta a 2023. Ana fatan Tinubu ya goyi bayan matashi da mutane daga lunguna da sakuna ke so kamar Yahaya Bello ya zama shugaban kasa a 2023."

Kara karanta wannan

Matasan APC a arewa sun bayyana wanda suke so ya gaji Buhari daga kudu maso gabas

Magaji ya shawarci Ganduje ya rike girmansa

Har wa yau, Magaji ya shawarci gwamnan na Kano ya mutunta kansa ya dena furta kalaman da za su ci karo da abin da mafi yawancin yan Najeriya ke so, na goyon bayan Yahaya Bello, rahoton The Sun.

Ganduje, a baya-bayan nan ya ce dukkan arewa na goyon bayan Tinubu a yunkurinsa na zama shugaban kasa a 2023, ya kara da cewa lokaci ya yi da arewa za ta yi wa Tinubu sakayya saboda goyon bayan Buhari a lokacin takararsa.

Buhari: Da zarar na kammala wa'adin mulki na zan koma gona ta a Daura in tare

A wani labarin, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya na da kudirin komawa gonarsa ta Daura, mahaifarsa da ke jihar Katsina, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban kasa ya furta hakan ne a Istanbul, kasar Turkiyya inda aka shirya masa bikin zagayowar ranar haihuwarsa ba tare da saninsa ba a ofishin jakadancin Najeriya da ke kasar.

Kara karanta wannan

2023: Na shirya kazamin artabu da kowa, babu abinda zai razana ni, Tinubu

Buhari ya na kasar Turkiyya yanzu hakan don halartar wani taro inda har ranar haihuwarsa ta zagayo, ya cika shekaru 79 kenan a ranar Juma’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

iiq_pixel