Jam'iyyar APC ta lallasa PDP, ta lashe kujerun ciyamomi da kansiloli a jihar Kebbi

Jam'iyyar APC ta lallasa PDP, ta lashe kujerun ciyamomi da kansiloli a jihar Kebbi

  • Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kebbi ta sanar da sakamakon zaɓen kananan hukumomi da ya gudana ranar Asabar
  • Shugaban hukumar KESIEC, Aliyu Muhammad Mera, yace jam'iyyar APC ta lashe baki ɗaya kujerun Ciyamomin jihar da Kansiloli
  • Tun da farko dai hukumar ta sanar da cewa jam'iyyu 18 ne zasu fafata a zaben 5 ga watan Fabrairu, amma daga bisani 17 suka fafata

Kebbi - Jam'iyyar APC ta samu nasarar lashe baki ɗaya kujerun Ciyamomi da Kansiloli a zaɓen kananan hukumomin jihar Kebbi da ya gudana ranar Asabar da ta gabata.

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kebbi, (KESIEC), ta sanar da cewa jam'iyyun siyasa 18 ne suka nuna sha'awar shiga zaɓen wanda ya gudana ranar 5 ga watan Fabrairu, 2022.

Daily Trust ta rahoto cewa hakan ba ta faru ba, inda a ranar zaben aka ga jam'iyyu 17 ne zasu fafata a kujerun kananan hukumomi da Kansiloli.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotu ta yanke hukunci kan sauya shekar Gwamna Matawalle zuwa APC

Taswirar Kebbi
Jam'iyyar APC ta lallasa PDP, ta lashe kujerun ciyamomi da kansiloli a jihar Kebbi Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Yadda sakamakon zaɓen ya fito

Shugaban hukumar KESIEC, Aliyu Muhammad Mera, shi ne ya sanar da sakamakon zaɓen ranar Litinin, 7 ga watan Fabrairu, kamar yadda The Nation ta ruwaito

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Muhammad Mera, ya bayyana cewa jam'iyyar All Progressive Congress (APC) ita ce ta samu nasarar lashe kujerun Ciyamomi 21 da kuma Kansiloli 225 dake faɗin jihar.

A jawabinsa, shugaban hukumar zaɓen ya ce:

"Duba da sakamakon da muka tattara, wanda aka bayyana a matakin gunduma a karamar hukuma, ina mai sanar da cewa jam'iyyar APC ta lashe kujerun Ciyamomi 21 da Kasiloli 225."

Zaben wanda ya gudana a baki ɗaya runfunan zaɓe dake kananan hukumonin jihar Kebbi, babu tashin hankali da rikicin siyasa, a cewar wasu rahotanni.

A wani labarin na daban kuma Malami ya bayyana shirin da Buhari ke yi na fallasa sunayen masu ɗaukar nauyin ta'addanci

Kara karanta wannan

Ya kamata PDP ta karɓe mulkin Najeriya, zaman lafiya ya gagara, inji gwamnan PDP

Ministan Shari'a ya roki yan Najeriya su ƙara hakuri game da fallasa sunayen masu ɗaukar nauyin ta'addanci a Najeriya.

Abubakar Malami ya tabbatar wa yan ƙasa cewa nan da yan makonni ma su zuwa za su yi farin ciki game da lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel