Sule Lamido: Ba ni tabbaci idan har yanzu Jonathan dan jam'iyyar PDP ne
- Goodluck Jonathan a matsayin sa na dan jam'iyyar PDP ya dade baya halartar manyan tarukan jam'iyyar gaba daya
- Tsohon shugaban kasar ya na kai wa Buhari ziyara a Aso Rock a kai-akai inda suke ganawar sirri, babu wanda ya san abinda suke tattaunawa
- APC ta bai wa tsohon shugaban damar fitowa takarar shugaban kasa a Jam'iyyar a 2023, inda shugabannin PDP suka zargi na APC da son birge Jonathan
Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan a matsayin sa na dan babbar jam'iyyar adawa ta PDP.
Jonathan ya kwashe tsawon shekaru a matsayin sa na dan jam'iyyar PDP tun shekarar 1999 amma sai dai kwanan nan, ba a ganin tsohon shugaban kasan a mahimman tarukan jam'iyyar, wanda ya hada da taron jam'iyyar PDP inda aka zabi Sanata Iyoricha Ayu a matsayin shugaban jam'iyyar na kasa.
A matsayin sa na shugaban kasa mai mulki, Jonathan ya rasa mulkin sa ga shugaban kasa Muhammadu Buharin jam'iyyar APC, Daily Trust ta ruwaito.
Ya amsa kaye a zaben, inda ya taka rawar ganin ya kawo zaman lafiya a kasashen yammacin nahiyar Afirika.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sai dai, an samu labarin cewa jam'iyyar APC ta na kokarin ganin ta tsaida shi a matsayin dan takarar shugaban kasa a shekarar 2023.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Jonathan ya na yawan kai wa Buhari ziyara a Aso Rock, inda suke tattaunawar sirri.
Tattaunawar sirrin da biyun suke da tarbar da Jonathan ya yi wa shugaban jam'iyyar APC a mazaunin sa ya janyo musayar yawu tsakanin shugabannin PDP da na jam'iyya mai mulki.
PDP ta zargi APC da son birge Jonathan, yayin da APC ta ce tsohon shugaban kasan ya na da damar takara a jam'iyyar a 2023.
Tsohon shugaban kasar bai halarci taron jam'iyyar PDP ba, wanda aka nada Sanata Iyoricha Ayu a matsayin shugaban jam'iyyar na kasa.
Yayin tattauna da BBC, an tambayi Lamido idan har yanzu Jonathan dan jam'iyyar PDP ne, amma tsohon gwamnan ya ce, "Ina tantamar hakan, ya jima ba ya shiga al'amuran jam'iyyar da ake gudanar wa kwanan nan."
Haka zalika, Lamido bai yi nauyin baki ba yayin da shugabannin jam'iyyar PDP suka kaiwa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ziyara, inda ya ce, sun zo ne don su nemi mafita mai dorewa ga matsalolin da kasar ta ke fuskanta.
Ya ce, "Tun lokacin da Buhari ya amshi mulki, Najeriya ba ta kara samun natsuwa ba saboda gwamnatin ta tarwatsa duk matakan da PDP ta kawo na cigaba.
"Ba mu da kwanciyar hankali, hadin kai, daraja, rikon amana kuma akwai tabbataccen talauci, saboda haka muna so mu canza wadannan abubuwan. Shiyasa muka yanke shawarar mu zo mu samu Obasanjo don yin hakan. Mun kai a kalla awa biyu muna tattauna wa da shi."
Shugaba Buhari ya yi ganawar sirri da Goodluck Jonathan
A wani labari na daban, jaridar Daily Trust ta ce, shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba 6 ga watan Oktoba ya yi wata ganawar sirri da tsohon shugaban kasa, Dakta Goodluck Jonathan, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Legit.ng ta tattaro cewa ba a san dalilin ziyarar ba saboda Jonathan bai yi magana da manema labarai ba bayan taron.
Sai dai kuma, an lura cewa tsohon shugaban, a matsayinsa na wakilin ECOWAS na musamman a Mali, yana ta yin taro akai-akai tare da Shugaba Buhari kan kasar ta Yammacin Afirka da ke fama da rikici.
Asali: Legit.ng