Wasu miyagu suna son raba ni da rayuwa ta, gwamnan APC ya yi korafi

Wasu miyagu suna son raba ni da rayuwa ta, gwamnan APC ya yi korafi

  • Gwamna Dapo Abiodun na Jihar Ogun ya koka a ranar Laraba, inda ya ce yanzu haka wasu ‘yan ta’addan suna son ganin karshen sa tun bayan kaddamar da shirin yaki da ta’addanci da gwamnatinsa ta yi
  • A ranar 21 ga watan Janairun 2022 gwamnatin Jiharsa ta kaddamar da wani shirin jami’an tsaro na hadin-guiwa, mai suna OP-MESA inda zai ayi amfani da shirin wurin yakar masu garkuwa da mutane da ‘yan damfarar yanar gizon Jihar Ogun
  • Sai dai yayin da gwamnan ya ke jawabi ranar Laraba a Abeokuta, ya ce bayan ‘yan ta’addan jiharsa sun ga yadda ya kaddamar da shirin shiyasa suka fara rura masa wuta kafin ya kawo karshen su

Ogun - Gwamna Dapo Abiodun na Jihar Ogun a ranar Laraba ya ce ‘yan ta’adda sun fara bin sawunsa inda suke farautar ransa duk saboda ya kaddamar da shirin kawo karshen su a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Ɗan Sanda Ya Bindige Soja a Fadar Shehun Borno

A ranar 22 ga watan Janirun 2022 Abidun ya kaddamar da shirin hadin gwiwa jami’an tsaro a jiharsa, wanda ya sa wa suna OP-MESA inda ya ce za su yaki duk masu garkuwa da mutane da kuma ‘yan damfarar yanar gizo.

Wasu miyagu suna son raba ni da rayuwa ta, gwamnan APC ya yi korafi
Gwamnan APC ya ce wasu miyagu suna son su kashe shi. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Sai dai a ranar Laraba yayin jawabi a Abeokuta, gwamnan ya koka akan yadda ‘yan ta’addan suka lura da shirin nasa suka fara rura masa wuta.

Gwamnatin Jihar Oyo da Ogun sun hada kawunan su wurin kafa shirin OP-MESA

Kamar yadda ya bayyana a taron jami’an tsaron hadin-gwiwa na Oyo da Ogun, wanda gwamnonin jihohin suka shirya musamman don kawo karshen ta’addanci a yankunan su, ya ce sun fara addabar rayuwarsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa suna farautar ransa saboda ya gallabi rayuwarsu.

Sai dai ya yi musu barazana inda yace jiransu kawai yake yi.

Kara karanta wannan

Obasanjo: Sai an binciko kuma an hukunta wadanda suka banka wa gona ta wuta

Abiodun ya kada baki ya ce:

“Bayan kaddamar da shirin OP-MESA a makon da ya gabata, na fahimci cewa suna iyakar dagewar su, kuma ina son in ji suna bayyana yadda na takura wa rayuwarsu.”

Gwamnan Abiodun ya ce ya kosa ya fara jin kukan ‘yan ta’adda

Daily Trust ta ruwaito inda ya ce:

“Na kosa in ji suna cewa Dapo Abidun ya takura mana. Don haka ina mai tabbatar muku da cewa sai na wahalar da su. Ina kuma jiran su.”

Yayin bayani a taron, Abiodun ya nuna yadda garkuwa da mutane da sauran laifuka suka zama ruwan dare a jihohin, wanda hakan yasa suka hada guiwa wurin kawo karshen su.

Ya kara da cewa duk jihohin suna fama da matsalar tsaro kuma suna ta aiki tukuru wurin shawo kan su.

Ya ce jami’an tsaron hadin gwiwar za su taimaka wurin inganta tattalin arzikin jihohin masu makwabtaka da juna.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Likitan Bello Turji da ke masa jinya da kawo masa kwaya ya shiga hannu

Gwamnan Jihar Oyo ya ce ya kamata a samar da ‘yan sandan jiha

Gwamnan ya ce bayan kaddamar da shirin OP-MESA, ‘yan ta’addan suna ji a jikinsu.

A bangaren gwamnan Seyi Makinde ya ce jami’an tsaron hadin-gwiwar suna da matukar muhimmanci kuma za su taimaka wa jihohin kwarai.

Gwamnan Jihar Oyo ya ce da shi da Abiodun za su ci gaba da yaki da ta’addancin da ya addabi jihohin su duk da bambancin jam’iyyun su.

A cewarsa samar da ‘yan sandan jiha yana da matukar muhimmanci kuma tushe ne na kawo karshen rashin tsaro.

Buhari: Na Ji Daɗin Yadda Masu Hannu Da Shuni Suka Gane Cewa Canja Najeriya Ba Aikin Mutum Ɗaya Bane

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya yi farin cikin sanin cewa kusoshin Najeriya sun gane cewa canja kasar nan aikin kowa ne, The Cable ta ruwaito.

Kamar yadda kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya bayyana a wata takarda, Buhari ya yi wannan furucin ne a ranar Lahadi a wata liyafa ta girmama shugabannin kwamitin kasuwanci, siyasa, kafafen watsa labarai da sauran ma’aikata.

Kara karanta wannan

Fasto ya rabo matar aure da 'ya'yanta mata 2 daga gidan miji, ya kawo su gidansa yana lalata da su a Ogun

Dama a watan Janairun 2021 The Cable ta bayyana yadda Buhari ya zargi masu fada a jin kasar nan da kawo cikas ga gwamnatin sa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164